Talla

Ɗalibi ya ɗaba wa malamarsa wuƙa har lahira

 Daga: Bello Hamisu

ABUJA, NAJERIYA - Wani ɗalibin makarantar sakandare ya ɗaba wa wata malama yar ƙasar Sifaniya wuƙa har lahira a wata makaranta a garin Saint-Jean-de-Luz na ƙasar Faransa.

Ɗan sanda mai shigar da ƙara na yankin, Jerome Bourrier ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na AFP harin, inda kafafen yaɗa labaran ƙasar suka ce lamarin ya faru ne a cikin aji a safiyar ranar Talata.

Hukumomi sun tabbatar da cewa ‘yan sanda suna wurin tare da mai gabatar da ƙara na yankin.

Rahotanni sun ruwaito cewa an kama ɗalibin.

Malamar tana da shekaru hamsin kuma ta mutu sakamakon bugun zuciya lokacin da jami’an agajin gaggawa suka isa wurin, kamar yadda kafafen yada labaran ƙasar suka bayyana.

Ministan ilimi na Faransa yana kan hanyarsa ta zuwa garin na Saint-Jean-de-Luz.

Post a Comment

0 Comments