Daga: Mohammad Abdallah
ZAMFARA, NAJERIYA — 'Yansandan Najeriya reshen Jihar Zamfara da ke Arewacin ƙasar sun kashe wani shahararren ɗan fashin daji sannan kuma suka kama wasu ɓarayi guda shida da ake zargi da fashi da kuma satar shanu. An ji haka ne ta bakin rundunar ‘yansandan jihar.
Kakakin ‘yansandan Jihar wato SP Muhammad Shehu wanda ya gabatar da waɗanda ake zargin a ranar Laraba, ya ce dakarun sun ƙwace bindiga ƙirar AK-47 biyu, da fakitin harsasai biyu, da tarin layu, da sauransu.
Ya ƙara da cewa,
"A ranar 1 ga watan Janairun 2023, rundunar ta samu wani rahoton gaggawa kan 'yan fashin daji a yankin Gusau da Magami da Dansadau. 'Yansanda sun isa wurin kuma suka far wa 'yan bindigar.
Ya ci gaba da cewa,
"Cikin sa'a, an kashe ɗaya daga cikinsu kuma aka daƙile harinsu, amma wasu sun gudu daji da raunukan bindiga."
Haka nan, 'yansandan sun yi nasarar kama wani da ke da alaƙa da jagoran 'yan fashi wato Halilu Kacalla shi kuma sunansa Musbahu Aminu.
SP Shehu ya ce, matashin mai shekara 30 ya amsa laifin aikata fashi da makami da satar shanu masu yawa a yankin.
Garuruwan Katsina, da Zamfara da Sokoto da Kaduna na ɗaya daga cikin garuruwan da suke fama da hare-haren ɓarayin daji masu satar mutane don karɓar kuɗin fansa.
1 Comments
Allah ya ƙara tona asirin azzalumai.
ReplyDelete