Daga: Mohammad Abdallah
KANO, NAJERIYA — Rundunar 'Yan Sandan Najeriya reshen Jihar Kano ta ce ta kama mutum 61 da take zargi da daba ko kuma jagaliyar siyasa yayin tarukan yaƙin neman zaɓe.
Kwamashinan 'Yan Sanda Mamman Dauda ya bayyana haka cikin wata sanarwa da kakakinta a jihar, a shafinsa na fesbuk SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ranar Alhamis, yana mai cewa an kama su ne a ranar Laraba.
Ya ce, An kama matasan ne a Filin Wasa na Sani Abacha yayin wani taron siyasa.
Ya ƙara da cewa daga cikin kayayyakin da aka ƙwace daga hannunsu akwai wuƙa 33, da takobi takwas, da almakashi huɗu, da kuma ƙunshin tabar wiwi 117.
Ya ci gaba da cewa,
"Shugabannin jam'iyyu da 'yan takara sun yi alƙawarin za su bai wa 'yan sanda haɗin kai da sauran jami'an tsaro don gudanar da zaɓuka cikin kwanciyar hankali," a cewar sanarwar.
Dama can garin Kano na ɗaya daga cikin garuruwan dake fama da jagaliyanci da daba da sara-suka da kwacen waya da kisa da sata da sane, kodayake jami’an tsaro da al’umma na iyakacin ƙoƙarinsu don ganin an shawo kan matsalar.
0 Comments