Daga: Arewa News
TARABA, NAJERIYA - Wasu da ake zargi 'yan bindiga ne sun kashe mutane fiye da biyar sun kuma ƙona rugage sama da goma sha a wani ƙauye da ake kira da Ngura dake a ƙaramar hukamar Yorroo a jihar Taraba.
Wani ganau da abun ya faru a gabansa mai suna Ardo Ummar Bello ya shida cewa ƴan bindigar sun zo ne da makamai su ka fara kashewa da ƙone duk abinda ya tari gabansu har su ka kona gidaje a ƙalla sha biyar da kuma kashe mutane fiye da biyar. Bayan wannan kuma sun ƙona kayan amfanin gona da aka noma a ƙauyen.
Wani wanda ya shaida faruwar al'amarin mai suna Hassan Abdullah ya ƙara da cewa, mahaifinsa ne aka kashe kuma ɓarayin sun tafi da gawarsa. Ya ce suna cikin halin tashin hankali na rashi samun gawar mahaifin nasa.
Alhaji Abdu wani ɗaya daga cikin wanda lamarin ya faru a idonsa ya ce, suna cikin mawuyacin hali wanda basu taɓa ganin irinsa ba tun da suke duniya kuma sun yi ƙoƙari sanar da hukumomi na jihar Taraba, amma kawo yanzu dai shiru ka ke ji ba wani labari domin ganin an kawo masu ɗauki.
An yu ƙoƙarin jin ta bakin jami'an dake yankin, amma har yanzu dai ba a samu ba.
Garuruwan Katsina da Kaduna da Zamfara da Sokoto da Taraba na daga cikin karuruwan da ɓarayin daji suka matsa mawa.
0 Comments