Talla

Wasu Matan Aure Sun Faɗa Shan Ruwan Akurkura dake Sa Maye A Kano

Daga: Abdullahi Abubakar

KANO, NAJERIYA — Hukumar dake yaki da fatauci da shan miyagun kwayoyi a Najeriya wato NDLEA, ta ce wasu matan aure sun faɗa harkar shaye-shaye wanda ya zama babban ƙalubale ta fuskar tarbiya da zamantakewa da kuma auratayya a jihar Kano.

Hukumar NDLEA ta ce tana fama da ƙalubale masu ɗinbin yawa, amma ta ce ofishinta na shiyyar Kano ya kama miyagun kwayoyi da wasu kaya masu sanya maye wanda suka kai kilo gram dubu takwas, haka kuma Jami’anta sun cafke mutane da ake tuhuma da ta’ammali da miyagun kwayoyi dake sanya maye sama da dubu daya a cikin shekarar nan 2022 da ta shude.

Abubakar Idris Ahmad shine kwamandan ofishin Kano na hukumar ta NDLEA dake yaƙi fatauci da shan miyagun kwayoyi a Najeriya, ya yi ƙarin bayani a kan wani sinadarin ruwan kwalba da ake yiwa laƙabi da “Akurkura” wanda ya fara zama ruwan dare a watannin bayan a jihar Kano, mutane na amfani dashi saboda wai an ce yana maganin cututuka da dama a jikin ɗan adam, duk da cewa yakan gusar da hankalin wanda ya yi amfani dashi.

A cikin wani jawabinsa ya ce,

“Sakamakon binciken da muka gudanar a dakin gwaje-gwajen mu na kimiyya dake shalkwatar hukumar mu a can Abuja, ya nuna akwai sinadarin tabar wiwi a cikin wannan ruwa na Akurkura. A don haka yanzu hukuncin Akurkura daya dana taba rwiwi, kamar yadda hukumar lafiya ta duniya ta ayyana”

Bayan la’akari da irin waɗannan sabbin ababen sanya maye ne masu kula da lamura ke ganin lokaci ya yi da ya kamata a yi garanbawul ga dokar data kafa hukumar ta NDLEA domin fadadawa da kuma inganta hurumi da ayyukanta.

Mohammed Ali Mashi, wani mai bibiyar ayyukan yaƙi da shaye-shaye a Najeriya, ya kawo shawarar cewa, ya dace majalisar dokoki ta Najeriya ta yi kwaskwarima ga wannan doka ta hukumar NDLEA.

An samu mata da dama waɗanda suka faɗa harkar shaye-shaye da yin amfani da akurkura wanda ke gusar da hankali, wasu masana ma sun ce ruwan na akurkura yana haɗe da sinadarin tabar wiwi wadda aka haramta amfani da ita a ƙasar Najeriya dama wasu ƙasashe da dama a faɗin duniya.

Post a Comment

0 Comments