Talla

Ko ganawar da tinubu ya yi da gwamnoni 5 na PDP zai taimaki APC ta lashe zaven 2023

Daga: Bello Hamisu

ABUJA, NAJERIYA — Kodayake, Jagoran ya musanta cewa ya gana da gwamnoni guda biyar a London. ɗan takarar jam’iyyar APC wato Bola Ahmed Tinubu ya musanta cewa ya gana da wasu gwamnoni na Jam’iyyar PDP.

Ya yi wannan bayanin ne a wata sanarwa da mai magana da yawun ɗan takarar APC mai suna Tunde Rahman ya fitar, a cikin sanarwar, ya ce, wasu ne kawai suka ƙirƙiro labarin don ƙudirinsu na siyasa.

Rahman ya ƙara da cewa, Tinubu na da ‘yancin ganawa da duk wani gwamna ko ƙungiyar da ya ke so don ya ƙarfafa siyasarsa.

A wani labari da aka samu wanda ya yi ƙarin haske inda ya ce, madugun gwamnonin 5 wato gwamnan jihar Riɓers Nyesom Wike, ya musanta labarin cewa sun gana da Tinubu a lokacin da ya dawo Najeriya daga London.

Dan kwamitin gudanarwa na APC Dattuwa Ali Kumo, wanda shi ma ya na London a lokacin, ya ce in Allah ya yarda nan ba da daɗewa ba waɗannan mutanen da ma wasu manya na jam'iyyar PDP za su fito su bayyana goyon bayansu ga ɗan takararsu na jam'iyyar APC.

Labarin da ya karaɗe kafafen sada zumunta wanda ya bayyana cewa ɗan takarar shugaban ƙasa ya samu goyon bayan wasu gwamnoni ya ja hankali inda ya tada ƙura a cikin jam’iyoyi masu hamayya da juna.

Manyan jam’iyyun hamayyar da suka fi ƙarfi su ne, APC da PDP da ANPP da kuma jam’iyyar LP, waɗannan jam’iyyu su ne waɗanda suka fi shuhura a kakar siyasa ta bana, kuma a cikin su ne aka sa ran samun shugaban ƙasa.

Al’umma dai na ta faɗin albarkacin bakinsu game da musantawar da Tinubu ya yi.


Post a Comment

0 Comments