Daga: Muhammad Abdallah
BAUCHI, NAJERIYA — Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Muhammed, ya
umarci al’ummomin jihar hallata hukuncin kisa ga masu garkuwa da
mutane da ‘yan ta’addan da suke yankunansu. Gwamnan ya yi wannan ikrari ne a
garin Rimi dake yankin karamar hukumar Alkaleri. Gwamnan ya yi wannan
umarnin ne a lokacin da yake jajanta masu bayan an kashe mutanen su fiye da
goma sha biyu da wasu ‘yan bindiga sukayi.
Daga cikin wadanda suka raka
Gwamnan akwai kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Bauchi Aminu Alhassan, inda suka
ziyarci ƙauyukan
Rimi, Mansur da kuma Yelwan Duguri.
A jawabinsa ga al’ummomin kauyukan CP, Aminu Alhassan, ya ce shi
da sauran abokan aikinsa jami’an tsaro ne suka fatattaki ‘yan bindigan.
A nasa jawabin Gwamnan Bauchi
Senata Bala Abdulkadir Muhammed, ya jinjinawa jami’an tsaro game da kokarin da
suka yi, kuma ya bada tabbacin bada tallafi ga iyalan da suka rasa ‘yan uwansu,
sannan ya bada umurnin a kashe duk wani ‘dan ta’adda da akayi ido biyu dashi.
Shugaban ƙaramar
hukumar Alkaleri na riko, Comrade Ibrahim Bala Mahmood, ya bayyana jin daɗi dangane da ziyarar da Gwamnan da
kuma tawagarsa suka kawo don jajanta musu game da abin da ya same su.
0 Comments