Daga: Bello Hamisu
Bisa wani bincike
da masana a ɓangaren tsaro suka yi, sun
gano cewa an ƙara samun yawaitar ‘yan bindiga da maraha da kashe mutane a faɗin
ƙasar Najeriya, kodayake jami’an gwamnati da hukumomi na ƙara kaimi wajen daƙile
ayyukan ta’addanci. Masanan da suka yi wannan bincike sun buƙaci
hukumomi a Najeriya su ƙarfafa haɗin kai tsakanin gwamnatoci don inganta yaƙi
da ayyukan ƴan bindiga masu addabar ƙasar Najeriya da
al’ummar dake cikinta.
Bayan wannan
kuma, sun buƙaci mahukunta su inganta tsarin tafiyar da tsaro ta yadda ba za a
samu giɓin da zai addabi al’umma ba.
Waɗannan shawarwarin na cikin rahoton
da wani kamfanin tsaro mai suna Beacon Consulting ya fitar inda ya ƙiyasta cewa
an samu ƙaruwar kashe-kashen mutane sanadin hare-haren da ƴan bindiga ke kai wa
a sassan ƙasar cikin watan Nuwamban da ya wuce.
Kamar yadda
rahoton ya bayyana ya ce,"An samu ƙari na yawan mace-mace da suka zarce kashi 50% daga watan
Oktoba zuwa Nuwamban bana".
Shugaban Kamfanin wato Dakta Kabir
Adamu ya ƙara da cewa, “Talauci ne kan gaba wanda ya taimaka wajen kawo
matsalar tsaro a Najeriya”
A cikin bayaninsa
ya kawo misali da wani rahoto da hukumar
ƙididdiga ta Najeriya ta fitar game da hasashen mutanen da ke fama da
talauci da ya kai miliyan 330 inda ya ce mafi
yawan lokaci ‘ƴan bindigar na amfani da talauci wajen tabbatar
da manufofinsu.
Dakta Kabiru Adamu ya
ƙara da cewa, duk da ƙokarin da gwamnati take yi wajen
dakile hare-hare a ƙasar, har yanzu ƴan bindiga na bin waɗansu hanyoyi suna
samun kuɗi sannan kuma suna faɗaɗa ayyukan ta’addancinsu.
Ya kuma
ce,
"Wani rahoto daga ɓangaren da ke
sa ido kan yadda ake tallafawa ko ɗaukar nauyin ta'addanci, rahoton ya nuna
cewa akwai wata ɓaraka da ƴan ta'adda ke amfani da shi
wajen samun kuɗaɗe."
Hare-haren ɓarayin daji dai na ɗaya
daga cikin abubuwan da suka hana raba dubban mutane da gidajensu sannan suka
raba tsakanin iyalai.
Wannan da ma wasu labarai ku biyo mu a
shafin www.arewanews.org.ng
0 Comments