Talla

Yan sanda sun kama matar da ta binne jaririn da ta haifa a Jigawa

 


JIGAWA, NAJERIYA_Rundunar 'yan sanda ta jihar Jigawa ta ce jami'anta sun kama wata mata mai suna Balaraba Shehu da ke ƙauyen Tsurma a ƙaramar hukumar Kiyawa bisa zargin binne sabon jaririn da ta haifa a ban ɗaki.

Yayin da yake tabbatar faruwar lamarin, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar DSP Lawan Shiisu Adam ya ce sakamakon bayanan sirrin da rundunarsu ta samu ne ya kai su ga gano matar tare da tono jaririn a ban ɗakin gidan.

''Bayan haihuwar ta ne sai ta shiga ban ɗaki ta haƙa rami a kusa da masai ta binne jaririn''

Ya ce bayan tono jaririn ne aka garzaya da shi babban asibitin Dutse inda likitoci suka tabbatar da cewa ya rasu.

DSP Shiisu Adam ya ce matar ta sanar da su cewa ta samu cikin ne ba ta hanyar aure ba, ta kuma bayyana wani saurayinta mai suna Ahmadu Sale wanda aka fi sani da 'Dan kwairo' da ta ce shi ne ya yi mata cikin,.

Kawo yanzu dai matar mai shekara 30 tare da saurayin nata mai shekara 25 suna hannun jami'an 'yan sanda.

Tuni kwamishinan 'yan sandan jihar ya bayar da umarnin mayar da batun zuwa shalkwatar cibiyar binciken manyan laifuka ta rundunar da ke babban birnin jihar Dutse.

Post a Comment

0 Comments