Talla

Yan Boko Haram sun Ƙona rumbunan hatsi da gidaje

Arewa News | Labarai

Daga: Bello Hamisu

BORNO, NAJERIYA -- Mayaƙan Boko Haram sun kai hari a wani ƙauye mai suna Jibwiwi dake ƙaramar hukumar Hawul a cikin Jihar Borno.

Maharan Boko Haram sun kai samamen ne aannan suka ƙona wasu rumbuna dake cike sa hatsi dangin gero da dawa da masara da wake da gyaɗa sannan suka ƙona gidaje da dama.

Bisa rahotannin da aka samu, sun ce an ƙona a kalla gidaje takwas da rumbunan hatsi waɗansa ke shaƙare da dawa da masara da sauran nau'ukan hatsi.

’Yan Boko Haram ɗin sun je ƙauyen ne a kan babura da yammacin ranar Litinin inda suka kai hari tare da ƙona gidajen.

Bayan nan kuma sun ƙona rumbunan sannan suka bar ƙauyen ba tare da sun ɗauki komai ba.

Wani dan kungiyar sintiri a ƙauyen ya shaida cewa, bayan mayaƙan sun ƙona gidaje da rumbuna a ƙauyen, sai suka wuce zuwa garin Ngulde da ke ƙaramar Hukumar Askira Uba, to amma sun murkushe su da taimakon mafarautar yankin.

Garuruwan Katsina da Zamfara da Sokoto da Kaduna dai na fama sa hare-haren ɓarayi masu satar mutane don karɓar kuɗin fansa.

Post a Comment

0 Comments