Talla

Yan bindiga sun kwashe mazajen wani kauye dake Zamfara

 Arewa News | Labarai


Daga: Bishir Ibrahim Idris

'Yan bindiga a Najeriya sun kwashe ɗaukacin mazajen garin Randa dake ƙaramar hukumar Maru a Jihar Zamfara saboda ɓacewar bindigoginsu, yayin da suka yi sanadiyar mutuwar 20 daga cikin waɗanda suka ɗauka. Rahotanni sun ce mabiya wani gawartaccen ɗan bindigar yankin da ake kira Lawali Damina ne suka aikata wannan aika-aikan na kwashe mazajen wannan gari, cikinsu harda ƙananan yara saboda ɓacewar bindigogin mabiyansa guda biyu.

A wannan yanki ne ‘yan bindiga ke sanya haraji da kuma ginɗaya shariɗoɗi ga jama’a a kan yadda za su gudanar da harkokinsu na yau da kullum. 

Wani Basarake dake kula da ƙauyen Randa, Abdulkadir Abdullahi ya shaidawa jaridar cewar tuni ƙauyen ya biya kuɗin kariyar da ƴan bindigar suka buƙata a ƙarƙashin Damina domin kaucewa kai musu hari. 

Bayanai sun ce a makon jiya ne aka fafata tsakanin mabiyan Damina da na abokan adawarsu a kan wata budurwa da ta ziyarci yankin daga Shinkafi, abinda ya kai ga kashe wasu daga cikinsu da kuma bacewar makamansu. 

Basaraken ya ce, wannan ne dalilin da ya sa Damina ya ziyarci garin, inda ya buƙaci yiwa mabiyansa jana’iza da kuma neman bindigogin da suka mallaka. 

Rahotanni sun ce rashin ganin bindigogin ya sa ya tafi da mutane 270 maza da suka haɗa da manya da kuma kananan yara. 


Basaraken yace sun shaidawa jami’an gwamnati halin da ake ciki amma babu wanda ya kai musu dauki. 


Ya zuwa wannan lokaci babu wani martani daga gwamnatin jihar Zamfara akan lamarin.

Post a Comment

0 Comments