Talla

Sojojin Najeriya sun ceto 'yan China bakwai daga hannun 'yan fashi

Daa: Muhammad Abdallah


Rundunar Sojan Sama ta Najeriya ta ce ta ceto 'yan ƙasar China bakwai da wasu 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a yankin Birnin Gwari na Jihar Kaduna.

Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce dakarunta na Tawaga ta 271 ne suka ceto mutanen a yau Asabar.

An sace su ne a watan Yuni da ya gabata lokacin da suke tsaka da aiki a wurin haƙar ma'adanai da ke Ajata-Aboki na Ƙaramar Hukumar Shiroro a Jihar Neja.

Sanarwar ta ce 'yan bindigar sun yi ta kansu lokacin da suka ga dakarun tawagar mai mutum 35 tsakar dare a yankin Kanfani Doka da Gwaska, inda suka bar 'yan Chinan da suka kama da kuma makamansu.

An kai su asibitin sansanin soja don duba lafiyarsu a Kaduna.

"Na ji daɗi sosai da ƙoƙarin da sojojinmu na musamman suka yi a Birnin Gwari da sauran wurare kuma ina da ƙwarin gwiwar nan gaba kaɗan za mu kakkaɓe duk 'yan ta'addan da ke yankin," a cewar Babban Hafsan Sojan Sama na Najeriya Oladayo Amao.

Post a Comment

0 Comments