MASHAWARTA NE MATSALAR: KADA A RUDU DA SHUGABA KADAI
Daga: Musa Bello Galadunchi
KATSINA, NAJERIYA - Duk kyawan manufofin shugaba, da tarin karatunshi, madamar na zagaye dashi ba al'umma ke gabansuba, to zaiyi wahalar gaske shugaban yayi abinda yakamata, akwai misalai barkatai akan haka
Ba kaga mulkin Yar'adua ba, na zagaye dashi sun taka muhimmiyar rawa wajen yin nasararshi, UWA UBA, shi Kuma daman mutumin kirkine
Amman yanzun da yake mafi yawan na tare da wannan gwamnatin ba al'umma ne gabanta ba, wane irin halin ni'yasu ne ba a gani ba, duka matakin jaha da matakin qasa
To haka, ko yanzun ba ta chanja zane ba, madamar shugaba zai zagaye kanshi da mutane marasa kishin al'umma sai kishin kansu da aljihunsu, babu abinda al'umma zata amfana daga irin wannan shugabancin sai lalacewa, talauci, kunchi da ci baya
Don haka, mu kula da kyau, ina? wane? dan takarane da party yafi tara mutanan kirki atare dashi, to mu karkata chan mu zabeshi, domin alamar juma'a, daga labara ake ganeta
Mun dai ga abinda jiya tayi, to kada muyi sakaci domin goben mu sai tafi MUNI
0 Comments