Talla

Majalisar Dattawan Najeriya ta Kasa Samun Matsaya a Kan Dokar da CBN ta Saka a Kan Ƙayyade Cire Kudi a ATM da POS

 Daga: Bello Hamisu

ABUJA, NAJERIYA — ‘yan masalisar dattawan sun kasa cin ma matsaya a kan sabuwar dokar cire kuɗi da CBN da kawo wadda ta ƙayyade yawan kuɗin da mutum zai iya cirewa a ATM da POS. A zaman da suka yi, majalisar dattawan sun yi tattaunawa mai tsawo a kan matsayar da kuma sabuwar dokar.

Wasu mambobin majalisar dattawan sun nuna goyon bayan dokar CBN yayin da wasu kuma suka nuna ƙin amincewa da sabuwar dokar cire kuɗi a ATM da POS.

Ta ɓangaren Shugaban kwamitin Sanata Uba Sani ya gabatar da wannan rahoto a zaman da majalisar ta yi na ranar Laraba, a wannan zaman Ƴan majalisar sun shafe tsawon sa'a'o'i suna tafka muhawara a kan batun cire kuɗi da kuma dokar da CBN ta saka.

Sanata Uba Sani ya gabatar da rahoton mai cike da rudani, wanda kuma 'yan majalisar suka yi ta jayayya a kai. Daga bisanin muhawarar da suka jima suna tafkawa ba tare da cimma matsaya ba, Majalisar Dattawan ta buƙaci a bayar da lokaci domin sake nazari kan shawarwarin da majalisar ta bayar.

Saidai Sanata Adamu Alero na daga cikin waɗanda suka goyi bayan wannan sabbin ƙa'idoji, ya yi ƙarin bayani a cikin majalisar indda ya ce,

“Ina ganin abin nan yana da amfani ga jama’a, kuma zai hana sayen ƙuria da kuɗi. Zai rage bayar da kuɗaɗe ga masu jefa ƙuria, kuma zai kawo tsafta ga siyasarmu.

Ya ci gaba da cewa,

“Saboda me? Saboda siyasar da ake yi ta kuɗi za ta rage har a zaɓi shugabanni kan cancantarsu ba saboda kuɗin da za su bayar ba.

Ya kuma ce,

“Ni na yi na’am da hakan. Idan kana da jama’a kuma suna sonka ka masu alheri ka mutunta su, to za a zaɓe ka. Idan kuma ba ka yi ba, ka ajiye kuɗi ko ka saci kuɗi don ka bai wa mutane, to kuɗin ba zai samu ba,”

Ta ɓangaren Sanata Adamu Muhammad Bulkacuwa daga Bauchi ta Arewa, ya ce akwai abubuwa da dama da aka bari a baya kafin aiwatar da waɗannan dokoki.

Ya ce,

“Ainihin gundarin tsarin idan har mun kai lokaci to yana da kyau, duk ƙasashen da suka ci gaba suna yin hakan. Amma a inda muke a yanzu a Najeriya, da yadda tattalin arziƙinmu yake to ba mu kai ba

Ya ce ƙasashen da suka ci gaba suna da wadatatun hanyoyin bin tsari, ya yi nuni da ceaw, ƙasaahen da suke bin irin wannan tsari, to duk tafiyar da za ka yi ta kilomita goma kawi banki a tsakani.

‘Yan Najeriya dai da dama suna ƙorafi a kan wannan sabon tsarin na cire kuɗi da bankin CBN ya kawo, da yawa daga cikin ‘yan kasa suna ganin yawan kuɗin ba za su isa buƙatoci ba, haka kuma an toshe hanyoyin samun kuɗi ga matasa waɗanda suke gudanar da sana’ar POS.

Wannan da a wasu labarai ku biyo mu a shafin www.arewanews.org.ng

 

 


Post a Comment

0 Comments