Daga: Arewa News
ABUJA, NAJERIYA — Ƙasar
Iran ta Rataye wannan mai rajin ƙin jinin gwamnatin mai suna Majid Reza Rahnavard
bayan yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya. Bayan shi akwai wasu masu
laifuffuka da aka yiwa hukuncin kisa ta hanyar rataya, wani ɗan ƙasar
da shima aka zarga da sa hannu a mutuwar wasu jami’an tsaro lokacin gudanar da
wata zanga-zanga da aka yi a watan Nuwamba.
Majid
dai ya daɗe a tsare yana jiran hukunci, saidai an yanke masa
hukunci ne bayan da kotu ta tabbatar da cewa yanad a hannu a kisan wasu jami’ai
biyu dake rundunar Basij, wannan runduna ta yi ƙarfin
suna wajen shiryawa da kitsa yadda za a kwantar da tarzoma a cikin ƙasar.
Ba shi
kaɗai aka yanke wa irin wannan hukuncin ba, ko a makon
da ya gabata, wata kotu dake Tehran ta yanke hukunci a kan wani mai suna Mohsen
Shekari wanda aka tuhuma da laifin taimakawa da kuma jigata wasu jami’an tsaro
a lokacin da suke ƙoƙarin kwantar da tarzoma tsaka da lokacin da ake
zanga-zangar.
Iran ta fada cikin rudani, tun bayan mutuwar matashiya Mahsa Amini
da ake zargin ta mutu saboda azabar da jami'an Hisbah suka gallaza mata bisa
laifin kin mutunta dokar sanya hijabi.
0 Comments