Talla

Kan Mage Ya Waye: Canza Sheƙa Baya Yaudarar Al'umma

 Daga: Musa Bello Galadunchi

KATSINA, NAJERIYA - A shekarun baya, duk irin lalatar da ɗan siyasa zai tabka, da zarar ya canza sheƙa ya koma jam'iyyar gwamnati ko mai farin jini, shike nan duk irin lalatar da ya shuka a baya to an yafe mashi. Yanzun kau ta canza zani, APC kun san da haka?

Wannan ne yasa ƴan siyasa suka rinƙa cin karensu babu babbaka; su handame dukiyar jama'a, su ƙarfafa wanda suke so, su karya wanda suke so, su musguna ma wancan, su taka wancan, sannan kai na cikin tukunya.

Sannan da sun ga zaɓe ya matso,  kuma jam'iyyarsu bata taɓuka komai ba, talakawa sun gaji da ita, za ai masu tawaye, sai suyi wuf su chanja sheqa, su koma jam'iyyar da ke da alamun cin zabe, kowa ya ga wannan babu adadi 

To yanzun kan mage ya waye, ba ruwan talakawa da duk inda zaka koma, duk Ka gama yawace-yawacenka, Kuma zabe yazo a rafka ka da ƙasa.

Ya ishe ku misali, abinda ya faru a zaben KANANAN HUKUMOMI A KATSINA, inda al'umma kaf, kwansu da Kwalkwata suka fito suka zabi PDP,  amman APC da RANA TSAKA, KATAA, ta sa karfin MULKI ta kwace zaben nan

To matsalar yanzun INEC tayi maganin wannan WASAN KWAIKWAYON, abinda duk ka shuka yanzun shi zaka girba.

Don haka APC kubar bata lokacinku, talakawa hakwanku suke, ku basu kudi su amsa, sannan su zabi abinda ransu yai masu, wato za a ga ramuwar gayya wallahi.

Kai bari ma in bar baku satar amsa, don kada ma ku ki fitowa da dukiyar da Kuka sace ku ba masu ita abinsu, domin dai ba zabenku zasu sake yiba

Ai jiki magayi, talakan zai sake kuskuren da yayi a 2015, ku sake maidashi cikin mugun halin da yafi wanda yake ciki yanzu!

Ko ba a fada maku ba, APC kin san baki saken cin zabe a Nigeria kaf, to balle Katsina, UWA UBA

Post a Comment

0 Comments