Daga: Musa Bello Galadunchi
Arewa News | Siyasa
Kada mu maimaita kuskure; zaɓin allah dai duk sadda za muyi magana mu ba Allah zaɓi, to sau nawa kaso abu amman ya zame maka musiba.
Ko sadda ni kaina na yi TAKARA ban taɓa cewa Allah ya bani ba, balle wani, sai gashi tun ba a je ko ina ba Allah ya nuna mani hakan shi ne mafi alheri, ni kaɗai na san abinda na gani.
Saboda haka, ina shawartar duk wani mai tallata Dan TAKARA, na kowa ne PARTY, ya rinƙa neman ZABIN ALLAH, a duk lokacin da zai yi magana a media da kuma boye.
Kada mu bari son kan mu ko buƙatar kan mu tasa mu yi MAKAUNIYAR SIYASA, mu sake maida kanmu cikin halin da ya wuce wanda muke ciki yanzu, kowa dai yana ji ajikin sa yanzu.
Domin ba lallai bane wanda kayi wa wahala a siyasa ya taimake ka bayan ya yi nasara, domin mafi yawansu ba su da halacci, mayaudara ne!
Kun ga wajen biyan buƙatar kanmu, sai mu jefa al'umma baki ɗaya cikin kunci, bala'i da musiba, kuma tamu buƙatar itama bata biya ba.
Saboda haka, mu ba Allah zaɓi cikin dukkan maganganinmu na KAMFE, ko Allah ya ji ƙanmu, ya bamu shugabanni na kwarai
Allah ya ba LADO da ATIKU nasara idan sune alheri.
0 Comments