Talla

In Dai Aiki Ake So: Katsinawa Sai Mai Karamin Karatu

Daga: Musa Bello Galadunchi

KATSINA NAJERIA - INDAI ZA AI MAMU AIKI, KATSINAWA SAI MAI 

KARAMIN KARATU

KARAMIN ilmi indai ana aiki dashi,  duniya ne malam.

Ka duba ka gani duk yawan masu PhDs din da aka tara a house of Reps, amman MURYAR GUDAJI KAZAURE KAWAI AKEJI  ALAJI, duk Ina masu Ph.Ds ?

Yo malam da dan boko akida; allazi boko, ba gara dan KASUWA BA, yo ina zaka hada wanda ke kama kudi kullun, da wanda sai karshen wata, MA'AIKATA ku guji wanda ke HANDAME BUDGET din shekara 4, wlh idan kuka fada hannunshi, sai dai Allah ya ceceku

Ina amfanin zunzuruntun KARATUN da baka iya maida TARO SISI dashi, Daktoci nawa ke garemu a jami'o'i, amman da aka shiga yajin aiki, wasu har mutuwa sukai tayi, saboda babu sana'a!

Amman ALAJI sai kaga drop outs yana hada albashin professors acikin wata daya, Kuma SECONDARY kawai gareshi, Kai a Borno State ma har Wanda ke kera mota aka samu, haba malam, kasan DAN KADAN mai ALBARKA, yafi tarin yawa na BANZA !!!

Nan Nan gida, kafin ma mu fita wata UWA DUNIYA, Wai ko kun manta da Dan Funtua, DAN KARAMIN CERTIFICATE amman sai afki, duk dan shekara 30 zuwa 40 yasan abinda nike nufi.

Yo wai malam kun manta ne, mafi yawanchin mutanen da suka SHAHARA anan cikin gida dama wajen, bafa wani KARATUN azo agani sukayi ba, KOFAR KWAYA, ta ishi kowa misali.

Tau ga Kuma giggan masu kudin duniya, wadanda duniya ke cikin amfanarsu yanzu haka:  irinsu Bilgate, da mai kudin AFRICA Dangote,da mai kudin DUNIYA, Elon Musk, duk mafi yawansu drop out ne fa, Kai malam, ka riqe Dan kasuwa kaji, Don ka tsira daga cin bashi !

SHA KURI KUNDUM, hatta inda nike wannan rubutun, wato a FACEBOOK, to mai shi drop out ne, shi ya fada da kanshi, Kuma sai kace ZUNZURUTUN KARATUN Ph.Dn da bai da amfani, yafi mai KARAMIN KARATU, to matsalar SHAYE-SHAYE kenan, idan mutum yasha, to komi zai iya fada, ko ya aikata.

Allah kada ka jarabemu da mulkin MASHAYA, DA ZUNZURUTUN KARATUN BOKO AKIDA.

Post a Comment

0 Comments