Talla

Ilimi Ne Yafi Ko Aiki da Ilimi Lado VS Ph.D Holder

 Daga: Musa Bello Galadunchi



Shin Iyayen mu tarin ilimi ne dasu, ko kuwa yawan aiki, baka buƙatar amsa, abin a  fili yake.

Shin mace mai tarin ilimi tafi biyayya ga miji, ko kuwa mai tsoron Allah, je ka tanbayi ma'aurata.

A cikin gidanku, ko a unguwarku mutane masu tsoron Allah suka fi yin abinda ya dace, ko masu tarin karatu?

Shin kai da ke fama da yunwa, rashin tsaro da talauci, wanda zai zo ya yi ta faman turanci kamar comrad ka ke so ko wanda zai zo ya zuba maka aiki ka ke nema?

Mata suna cewa da ki haifi Dan BOKO, gara ki haifa mashi mata.

Ku tambayi ma'aurata ku ji, shin gogaggiyar yar BOKO tafi biyayya koko yar bagidajiya-bagidajiya?

Shin mai dan karamin karatu wanda zai zuba mamu aiki shi yafi ko mai tarin karatu babu aiki shi yafi?

ZAƁI YA RAGE GA MAI SHIGA RIJIYA

Post a Comment

0 Comments