Talla

Don ba ka da Jam'iyya...

 Daga: Yakubu Lawal 

.....2015 zuwa yau...!!

KATSINA, NAJERIYA - Na zaɓi in fara rubutu na da wannan taken ne, saboda ganin yarda muka dabi'antu da la'akari da Siyasarmu, ƙabilarmu, Addininmu ko Danganenmu, wajen nazarin ire-iren wannan rubutun a kafafen sadarwa.

Na tsaya na yi nazarin cewa idan zamu aje Siyasa/Jam'iyar da muke ra'ayi (PARTISANSHIP) zamu ga cewa tun bayan dawowar mulkin dimokaradiya a wannan jamhuriyar, daga shekarar 2015 zuwa yau,siyasar Nijeriya ta bude sabon shafin da 'yan Nijeriya ya kamata su dauki darasin daidaita sahu don dorewar ita kanta Kasar da al'ummarta.

 Batu na farko da muka riska shi ne, ganin a shekarun da aka yi na dawowar mulkin dimokaradiya,shi ne a karon farko samun nasara da rinjaye mai yawa da babbar Jam'iyar adawa ta yi da sunan zabin da al'umma suke so,sannan aka mika mulki ga wadanda suka ci zabe ba tare da tada jijiyoyin wuya ba.

     Sai dai bayan nan, qalubale kala-kala suka kunno kai ga kusan dukkan bangaro na rayuwar masu mulkin da talakawa, a inda a yayinda masu mulki suke fama da rigingimun siyasa da kokarin kauda duk wani tarnakin daka  iya barazana ga kujerunsu da siyasarsu,wannan ya sanya wasu suka zabi ko dai canza gidajen siyasa ko Jam'iyar ma baki daya,to amman duk da kokarin kaucewa irin wadannan matsaloli har yau har kwanan gobe, wadannan matsalolin sune suka yi kaka-gida,suke ta bin masu mulkin da jam'iyun nasu. Inda har wannan lokaci da muke na saura 'yan kwanaki ayi babban zabe na Shekarar 2023,babu Jam'iyar da ta samu nasarar dinke barakokin da suke fuskanta ba.

 A dayan bangaren,talakawa suma na kusan dukkan bangarorin  kasarnan suna fuskantar daya daga cikin qalubalen da ka iya kawo tarnaki ga jin dadi da walwala  ta rayuwa,kama daga rashin tsaro,rikicin addini da siyasa,rikicin ta'addanci da na qabilanci da matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa da  makamantansu.

     Duk da wadannan matsaloli da har gobe ba su kauba ga masu mulkin balle ga talakawa,mulkin dimokaradiya daga shekarar 2015,ya kasance lokaci da gwamnatoci suka yi ayyuka na raya Kasa,da za a iya gani a nuna a dukkan mataakai na gwamnati a bai daya wato(UNiFORM INFRASTRUCTURAL DEVELOPMENT). Masu karatu za su yarda dani bisa ga cewa gwamnatin tarayya ta yi ayyuka dadama a bangarori dabam-dabam ko da cewa ayyukan ba su yi daidaida ra'ayinka ba, ko kuma ace ba a yi su inda ka ke so a yi ba. Kazalika gwamnonin Jahohi ma in muka yi masu kudin goro, ba tare da la'akari da Jam'iyar da suka fito ba,suma a jahohinsu sun yi rawar gani ta fuskar zuba ayyuka a Kasa. Masu karatu zasu ga wannan zance a fili da wannan misalan da zan yi da wasu Jahohin Nijeriya. Misali a Jahar Delta da Rivers,a Bauchi da Borno,sai Kano da Kaduna, ga mai bin kadin abubuwan da ka-je- su-dawo ,kadan ne daga cikin misalan tun kusan mafi rinjayensu sun tabukawar da ko da gwamnonin da suke mulkin ba ka ra'ayinsu a siyasance ka yaba da daya daga cikin ayyukan da suka yi koda kuwa ba bukatar al'ummar ba ce wannan aikin.

Wadannan misalan sun nuna cewar, daga shekarar 2015, akwai cigaban ayyuka a bai daya daga masu shugabanci da masu mukamai a jam'iyu dabam-dabam.

     Sai qalubalen can dana fadi a baya yafi tasiri a zukatan al'umma fiye da aikin da suke gani a Kasa,saboda dama duk al'ummar da ta rasa Zaman Lafiya,Ilmi da Lafiyar Jiki da ta Jikka,kusan komai aka yi akasin su, duk darajar sa zai zamar masu ga koshi ga kwanan yunwa.

Wani abin da ke da daure kai, ga wadannan matsaloli da suka ki ci suka ki cinyewa  shi ne,a kullum mahukunta batunsu shi ne suna bakin kokarinsu na ganin an ragewa al'umma/Talakawa radadin matsalolin da ke sha masu kai,su kuwa al'umma(Talakawa)kullum kokensu shi ne basu ji ba balle su gani,wannan ne ya sanya abubuwa suka cabewa masu mulki tare da ita Kasar baki daya,Musamman yanzu da duk shugaba ke bukatar yabo,ba fallasa ba.

Shin ko Ina Matsalar take.????????Ga FITILAR ko ga BATIR???


Alqalamin Yakubu Lawal 

Dan Jarida

Jami'in Hulda da Jama'a a Katsina.

Post a Comment

0 Comments