Talla

Cece-ku-ce tsakanin Jarumin Kannywood Sadiƙ Sani Sadiƙ da Malaman Addini ya ja masa Tofin Alatsine a Tiktok

Daga: Muhammad Abdallah



KANO, NAJERIYA Sharareen ɗan wasan Hausa mai suna Sadiƙ Sani Sadiƙ ya ja wa kansa tofin Allah tsine a wajen Malaman Addini bayan ya saki wani faifan bidiyo a kafar sadarwa ta tiktok.

A cikin faifan bidiyon ɗan wasan Fim ɗin wato Sadiƙ an ga shi a gaban wani gida sanye da wata shuɗiyar riga. A cikin bidiyon ya fara da jawo hankalin wasu malamai da suke fitowa a cikin kafar sadarwa ta Tiktok suna yin wasu abubuwa da yake ganin ba daidai ba ne. A cikin bidiyon ya yi zargin Malaman suna yin amfani da rigar addini suna yin kalaman da ba su dace ba na ɓatanci.

Sadiƙ ya sufanta wani malami daga Bauchi wanda ya ambaci wani malami ɗan uwansa da wani suna marar daɗi. Ya ƙara da cewa haka kuma, shi wannan malami da aka kira da suna marar daɗi ya yi raddi inda ya riƙa kiran sunayen wasu malamai waɗanda suka fi shi fikira da ilimi sannan ya riƙa yin maganganu maras sa daɗi da ɓatanci a kan su. Duk da haka shi wannan malami bai yi ɗarɗar ba, sai da ya sake fitowa a wani faifan bidiyo inda yake sukar masu shirya fina-finan Hausa.

A cikin bidiyon Sadiƙ ya yi karin bayani a kan yadda yake alfahari da sana’arsa ta fim inda ya yi iƙirari cewa, yana fata ya mutu a cikin har ka kuma zai tafi gaban Allah da sunan masu shirya fim, kuma yana fata idan yaransa sun taso su yi harkar fim ba tare da ya yi wata nadama ba. A cikin kalamansa ya ce,

“Ina alfahari ni ɗan fim ne, ina fata idan ‘ya’ya sun taso, suna da ra'ayi, su yi fim ɗin nan ba matsala ba ce a wajena, ina sa rai zan mutu in tafi gaban ubangiji a matsayin ɗan fim, insha Allah, bana nadama da wannan ba kuma taɓa nadama ba”

Bisa wannan sai sadiƙ ya yi zargin wancan malamin ya fito yana ƙalubalantar 'yan fim yana cewa, babu mai addini a cikin ‘yan fim, bisa wannan sadiƙ ya yi jan hankali da cewa duk da cewa a tarbiyar gidansu ba su zagin manyan mutane da suka zage su amma yana ba wannan malami shawara ya bar zagi tare da cin mutumcin duk wanda ya bi ta kansa, kuma yana roƙo Allah ya ba wannan Malami haƙuri.

Saidai wannan kalaman ya ja wa Sadiƙ Sani Sadiƙ tofin alatsine duk da cewa babu wasu kalamai na cin zarafi ko ambatar sunan wani malami a cikin kalamansa. Inda har wasu malaman addini suka riƙa fitowa a kafar sadarwa ta Tiktok suna zagi tare da tsinewa wannan ɗan fim ɗin wato Sadiƙ Sani Sadiƙ.

Duk da yake malaman a cikin karatuttukansu ne suka soki lamirin ɗan wasan Kannywood amma wasu ne ma’abota hawan kafar sadarwa ta Tiktok suke ɗauko maganganunsu suna ɗorawa don su samu mabiya. Wato dai kamar yadda aka riƙa ɗora karatuttukan waɗancan malaman da suka yi cacar baki, haka aka ɗauko nasa karatuttuka ana ɗorawa a kafar tiktok.

Tuni dai ake zargin mabiya wannan kafar ta Tiktok da yaɗa abubuwa masu kawo ruɗani a cikin al’umma a ƙasar Hausa har ma wasu na ganin cewa rufe kafar yafi alheri da alfanu fiye da barin ta.

Wannan da ma wasu labarai ku biyo mu a shafinmu na www.arewanews.org.ng

  

Post a Comment

0 Comments