Daga: Musa Bello Galadunchi
Arewa News | Siyasa
KATSINA, NAJERIYA - Hankalin duk wani mai ruwa da tsaki na APC ya tashi jiya, ganin taron da ba a taɓa gani ba na ɗan mutum, domin tarbar ATIKU DA LADO, taron da ya dugunzuma hankalin duk wani mai faɗa aji na jam'iyyar APC, ai na ji muryoyin wasu jiga-jigan APC na cewa 'kai wane, akwai fa matsala', ni kuma na kyalkyace da dariya nace, ba kuga komai ba.
Safkowa da ni ke yi in fito ɗan in sha iska saboda taron dubun-dubatar al'umma, sai na hango su o' o da aka zo ganin kwam, idan taron bai yi armashi ba, azo media ayi gogar zana, sai na ga sun sulale jiki ba kwari sun fice da takaici, shi yasa ka ji su yau tsit a media, saboda ciki ya ßuri ruwa.
Wata Majiya ma da nike samun labarai an ce yau tun da farar safiya aka tattara duk wani jigo a jam'iyyar domin zaƙulo hanyar da za a ɗinke barazanar da taron na jiya ya haifar, domin maganar gaskiya, an kwance ma APC zane a kasuwa jiya.
Ba Kuma kowa bane ya jagoranci wannan tonon SILILIN da aka yiwa APCn ba jiya illa madugun tafiyar tare da shugaban KAMFE na ATIKU/LADO wato Dr. Mustapha M. Inuwa, uwa uba gashi Kuma sun haɗe da KATAFILA SARKIN AIKI, wato Barrister Shehu Shema.
Kai gaskiya jiya ta bayyana a fili in dai zaɓen gaskiya za ayi, to duk wani ɗan PDP ya koma gida yai bacci har da saleɓa, domin jiya AREWA ta nuna al'ummar Nigeria cewa wannan karon magana ta korar APC, domin sun gaji da yunwa, talauci, rashin tsaro da sauran fitintinu da yankin da kuma ƙasa baki daya ta samu kanta a ciki, Wanda Kuma duk APCn ce sila.
To Katsina kaɗai kenan, Ina baku tabbaci abinda duk sauran jahohi za suyi kenan a zaɓe mai zuwa na 2023, idan Allah ya kai mu.
1 Comments
Wannan gaskiyane domin sunsan basu shuka abin alkairi da zasu tunkarar al'umma dashiba a kowanne yanki na kasarnan,
ReplyDeleteDanhaka in sha Allah PDP zatayi nasara awannan gaggarumin zabe mai zuwa na 2023