Talla

An Ƙwaƙulewa Almajiri Ido A Bauchi

 Daga: Muhammad Abdallah


KANO, NAJERIYA Wasu mutane da ba a san su ba sun yaudari wani almajiri a kusa da makarantarsu inda yake karatu, suka ɗauke bisa mashin da niyar zai nuna masu gidanw wata mata, suka kai shi bayan gari sannan suka cire masa ido da ƙarfin tsiya. Bayan nan ne sai yaron ya yi ƙarfin hali sannan ya fito inda ‘yan uwansa suka gan shi, daga nan ne sai aka ɗauke shi zuwa asibiti.

Bayan sanar da 'Yan sanda abinda ya faru, sun fara gudanar da bincike game da wannan hari mai tayar da hankali a kan almajirin wanda bai wuce shekara 12 ba, mugayen mutanen sun ƙwaƙule masa ido ɗaya. ‘Yan sandar Jihar sun fitar da sanarwa inda suka ce,

Wasu mutane baƙin fuska su biyu a kan mashin sun yaudari  wani almajiri suka kai shi bayan garin Kafin Madaki, da ƙarfi da yaji suka ƙwaƙule masa idonsa na dama. 'Yan sandan jihar Bauchi sun ce maharan da suka ƙwaƙule wa yaron ido sun yi tafiyar su, inda suka bar shi cikin jini a bayan gari.

Sanarwar mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Bauchi SP Ahmed Mohammed Wakili ta ce, yaron ɗan asalin jihar Kano ne kuma yana karatun allo  wata makaranta da ke Kafin Madaki lokacin da mummunan al’amarin ya faru a kansa ranar Juma'ar da ta wuce.

Sanarwar ta ƙara da ce, wurin da aka yi wa yaron aika-aikar ba shi da nisa da makarantarsu.

A cikin sanarwar ta ba da tabbacin cewa 'yan sanda na nan suna ƙoƙarin kama waɗanda suka aikata wannan ta’asar.

Babu masaniya kan abin da ya sa maharan suka ƙwaƙule idon yaron sai dai a 'yan shekarun nan ana samun rahotannin yadda ake cire sassan jikin mutane don yin tsafi. Ko a farkon wannan shekara ma, an cire wa wani yaro idanuwansa biyu a jihar ta Bauchi.

Wannan da ma wasu labarai ku biyo mu a shafinmu na www.arewanews.org.ng

 

 

 

Post a Comment

0 Comments