Daga: Muhammad Abdallah
SAKKWATO, NAJERIYA — Rundunar ‘Yan Sandar jihar ta gano wasu
makamai masu tsananin haɗari a wasu ofisoshin siyasa, an dai yi zargin cewa
makaman an ɓoye su ne don ayi amfani da su a kakar siyasa ta bana a jihar ta
Sokoto inda jam’iyyar PDP ke mulka.
Rundunar ‘yan sanda Najeriya ita ce ta bayya yadda ta gano makaman da aka boye a ofisoshin wasu
jam'iyun siyasa a Sakkwato. A Najeriya, duk sanda aka buga
gangar siyasa, mutane kan yi ta ɗarɗar saboda tsoron tashin hankulla da ake faɗawa
sanadiyar siyasar. Wasu lokutan kuwa har ana samun zubar da jini da kashe-kashe
da ƙone-ƙone da kuma asarar dukiyoyi a lokacin da kakar siyasa da kama. Wannan ne
yasa wasu ƙungiyoyi da hukumomi ke yin ƙoƙarinsu wajen ganin an magance rikicin
siyasa a cikin ƙasar.
Amma wannan
na kawo tirjiya saboda wasu jam’iyyun siyasar da suke ƙoƙari koda tsiya ko da
tsiya-tsiya sai sun sake ɗarewa bisa kujerun mulkinsu.
A jihar Sakkwato dake Arewa maso
yammacin Najeriya rundunar ‘yan sanda ta ce, ta kama makamai a ofisoshin wasu
jam'iyu da ake tarawa don yin ta'addanci.
Kwamishinan ‘yan sanda a jihar Muhammad Usaini Gumel ya ce, sun samu labarin ana tara makaman ne inda suka kai samame suka kama makamai a ofisoshin jam'iyun APC da PDP na ƙaramar hukumar Isa.
Yace makaman sun haɗa da adduna, sanduna, bindigar gargajiya ta harba ruga da sauran nau'o'in makamai.
Saidai har yanzu ƙungiyoyi da hukumomin gwamnati da jami’an tsaro basu yi ƙasa a guiwa ba wajen ganin sun kawo ƙarshen tashe-tashen hankulla a lokuttan zaɓe. Jami’an tsaro dake ƙasar a shirye suke su tunkari duk wata tarzoma da zata taso a kafin zaɓe da kuma bayan zaɓe.
Da yawa dai na jama'a musamman na yankunan da ke fama da rashin tsaro a Najeriya, ke ta tunanin yadda zabe zai gudana a yankunan su.
Wannan da ma wasu labarai ku biyo mu a shafinmu na www.arewanews.org.ng
0 Comments