Talla

Aisha Buhari ta Janye Ƙarar da ta Shigar kan Ɗalibi Aminu Muhammad

 Daga Arewa News

ABUJA, NIJERIYA _ Aisha Buhari wato matar Shugaban Najeriya ta janye ƙarar da ta shigar kan Aminu Muhammad, ɗalibi a wata jami'a dake Jigawa wanda ke gab da fara zana jarabawa, wani lauya ne dake kare ɗalibin ya shaida haka.

Cikin wani saƙon SMS da Lauyan mai suna Barista C.K. Agu ya.rubuta, babu cikakken ƙarin bayani a kan dalilin da ya sa Aisha ta janye ƙararta.

Ɗalibin dai ya shafe kwanaki a gidan yari bayan ya yi rubutun suka ga maiɗakin shugaban ƙasa a kafar sadarwa da Tuwita, bayan kotu ta tuhumi ɗalibin bai amsa laifin ya ake tuhumarsa ba, sai kotu ta aika da shi gidan yari na Suleja inda ya kwana har uku.

A ranar Litinin ake sa ran ci gaba da zaman kotun don sauraron neman beli da lauyan Aminu ya yi a zaman ranar Talata da aka yi, wanda bai yi nasara ba.

Matar shugaban na zargin Aminu da ɓata mata suna saboda saƙon da ya wallafa a shafinsa na Tuwita maƙale da hotonta tare da cewa "ta ci kuɗin talakawa".

Ƙungiyoyin kare haƙƙi da masu sharhi sun soki Aisha game da matakin da ta ɗauka bayan rahotanni sun yi zargin cewa sai da aka lakaɗa wa Aminu duka kafin gurfanar da shi a gaban kotun.

Wasu sun soki matashin kan zargin da ya yi wa matar shugaban.

Labarai | Arewa News

Post a Comment

0 Comments