Daga: Musa Bello Galadunchi
Arewa News | Siyasa
Tashin hankalinsu, shi ne kururuwa da ambaliya da jama'a za su yi wajen tarbar Atiku a Katsina, alama ta farko da ke nuna sun faɗi zaɓe sun gama.
Ai ko ɗan mutane su nuna haushin su da irin ƙagara da su kayi ranar zaɓe tazo, domin su yada kwallon mangwaro ko sun huta da ƙuda, wadɗnda ma ba su da niyar zuwa taron, suna faɗin sai sun je sun gane wa idonsu.
Kasan sun kware da farfaganda a media da almarar cewa Katsina ta Dikko CE da Tinubu, to sun san taron yau zai tona masu asiri, shi yasa tun farko suka hana ayi amfani da STADIUM ɗin, amma Gwankin naka LADO, ya tura mai girma DG wato dodon APC, Dr. Mustapha Inu ya je ya gamu dasu, yo KA ƘARA JIN MAGANAR, NAN TAKE SUKA BADA DAMA.
To yanzun dai ta faru ta ƙare, tun jiya al'umma ke ta KWARAROWO ta ko ina, abinda suke gudun ya faru, ba a zaɓe a social media, abinda APC ta kware dashi kenan, PDP tace mu gani a ƙasa.
Tabbas yau kowa zai gani aƙasa, mu ba a media muke KAMFE ba, na shata yace "YAWAN MUTANE SHI NE KASUWA, NI KU RABANI DA TARIN RUMFUNA".
2 Comments
Wannan gaskiyane Allah ya kawomana dauki ajahata dama kasa baki daya
ReplyDeleteMuna mai addu'ar da fatan samun nasara insha allahu.
ReplyDelete