Ƙungiyar ci gaban al'ummar Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna, BEPU ta ce ta damu ƙwarai tare da yin Allah-wadai kan kisan rubdugu da aka yi wa wasu mutum biyu da ake zargin makiyaya ne da ke da alaƙa da ƴan fashin daji.
Ƙungiyar ta BEPU ta nesantar da kanta da yadda aka kashe mutum biyun tare da gargaɗi kan cewa jama'a su daina ɗaukar doka a hannunsu idan ransu ya ɓaci inda ta buƙaci jama'a su rinƙa kai kokensu ga hukumomin da suka dace.
Haka kuma BEPU ta jinjina wa jami'an tsaro da ke ƙoƙarin tabbatar da tsaro a yankin na Birnin Gwari amma duk da haka ta nuna rashin jin daɗinta kan yadda ake bayar da rahotanni marasa daɗi kan Birnin Gwari inda ta ce wasu rahotannin za su iya jefa mazauna ƙaramar hukumar cikin hatsari.
BEPU ta ce gwamnati ta yi gaggawa wurin fitar da sanarwa ba tare da zurfafa bincike ba kan mutanen da aka kashe inda ta ce mutanen da ake zargin makiyaya ne ba makiyaya bane.
Ƙungiyar ta ce bisa bincikenta, waɗanda aka kashen da ake zargin makiyaya ne ba ma ƴan Najeriya bane inda ta ce masu ayyukan ta'addanci ne da suka zo daga Sudan waɗanda kuma suna daga cikin masu kai hare-hare a yankin na Birnin Gwari.
0 Comments