Talla

Joshua Dariye Zai Tsaya Takarar Sanata Bayan Ya Shafe Tsawon Lokaci A Kurkuku

Daga: Bello Hamisu

Abuja, Nigeria Tsohon Gwamnan Jihar Filato wato Joshua Dariye ya yi wani yunƙuri na sauya sheƙa don tsayawa takara a Jam’iyyar labour wadda Mr. Piter Obi zai yiwa takarar Shugabancin ƙasa. Yunƙurin nasa yana shan suka daga ‘yan ƙasa da kuma masu yaki da cin hanci da rasawa. Tsohon gwamnan dai wanda ya daɗe tsare a kurkuru bayan fitowarsa ya yi aniyar tsayar takarar kujerar Sanata ne a mazaɓar Filato ta tsakiya.

Gwamnan ya yi tsawon shekaru huɗu ɗaure a gidan matsa bayan wasu tume-tume da aka yi masa na almundahana da kuɗaɗe, a ranar litinin ne dai aka sako shi tare a wasu mutane.

Jim kaɗan bayan sakinsa aka fara yaɗa fitowa takararsa inda yake neman kujerar Sanata a Filato ta tsakiya, saidai mutane nata faɗar albarkacin bakinsu a kafofin sada zumunta musamman a kafar sadarwa ta fesbuk.

Jaridar TheGurdian ta ruwaito cewa, Jam’iyyar Labour Party (LP) a jihar ta bai wa tsohon gwamnan jihar Filato, Sanata Joshua Dariye da tsohon mamba a majalisar ministocinsa Alexander Kwapnoe tikitin takarar Sanata.  Yan takarar guda biyu za su fafata ne da kujerun sanatoci na Filato ta tsakiya da kuma Filato ta Kudu.

Dariye, wanda aka yi wa afuwa  kimanin watanni biyu da suka wuce, ya shaƙa iskar ‘yanci kwanaki kaɗan da suka wuce.

Dariye, wanda ya wakilci Filato ta tsakiya a zauren majalisar dokoki ta ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar LP tsakanin 2011 zuwa 2015 kafin ya koma APC, zai fafata da Diket Plang na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da Golkuna Gotom na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Plang ya lashe zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC wanda hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta sanyawa hannu a Jos.

Dariye, bayan an sake shi kwanaki uku da suka wuce, a Abuja, ya ce siyasa ta zama wani ɓangare na rayuwarsa; don haka ba zai iya barin siyasa ba.

Sai dai masu yaƙi dacin hanci da rashawa a Najeriyar na cewa, bai kamata a ba shi wannan damar ba, ganin cewa dawowarsa ke nan daga gidan yari, sakamakon ɗaurin da aka yi masa, bayan kotu ta kama shi da laifin cinye kuɗin jihar ta Filato a zamanin da yake gwamna.

Auwal Musa Rafsanjani wakilin kungiyar Transparency International a Najeriya ya bayyana cewa, wannan ya nuna cewa yaƙi da cin hanci da rashawa da ake yi a Najeriya ya zama wasan yara.

Ya ƙara da cewa "Idan Buhari ya ce ya yafe, ai jama'ar da aka sace kuɗinsu waɗanda suna nan suna fama cikin wahala da yunwa da talauci ai su ba su yafe ba,"

 An haifi Joshua Chibi Dariye a ranar 27 ga Yuli 1957, ya ɗare kujerar gwamnan jihar Filato ta Najeriya a ranar 29 ga Mayu, 1999 a lokacin zaɓen gwamnan jihar Filato a shekarar 1999 a ƙarƙashin jam'iyyar PDP. An sake zaɓe shi na tsawon shekaru huɗu tun daga watan Mayun 2003, kuma an tsige shi a watan Nuwamba 2006 duk da cewa kotun daukaka kara ta Najeriya ta soke tsige shi a ranar 27 ga Maris, 2007, hukuncin da Kotun Koli ta amince da shi. Dariye ya ci gaba da zama ofis na tsawon wa’adinsa.

Post a Comment

0 Comments