Talla

Yan bindiga sun sace Maigari da Ɗansa

 Daga: Mohd Abdallah

BAUCHI, NAJERIYA — Rundunar ƴansanda a jihar Bauchi da ke Najeriya ta tabbatar da kai hari tare da sace maigarin ƙauyen Zira mai suna Alhaji Yahya Abubakar da kuma ɗansa wato Habibu Saleh a ƙaramar hukumar Toro.

Mai magana da yawun rundunar SP Ahmed Wakil ne ya faɗi wannan sanarwar ga manema labarai.

Ya ce, ƴan bindigar sun shiga ƙauyen ne da misalin ƙarfe sha biyu na dare a ranar Lahadi sannan suka sace mutane.

Ya kuma ƙara da cewa, yanzu haka jami'an tsaro sun shiga cikin daji don neman inda aka ɓoye waɗanda aka sace.

Ya kuma ce,

"Muna bai wa al'umma tabbacin cewa za mu kwato waɗanda aka sace"

A cikin sanarwar an nemi haɗin kai daga al'ummar ta kuma neme su da su cigaba da hidimominsu.

Post a Comment

0 Comments