Daga: Arewa News | Hausa
A wata fira da aka yi da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya faɗi dalilin da yasa gwamnatinsa bata cire tallafin man fetur ba. Ya ce gwamnatinsa ta ji tsoron yadda rayuwa zata tsananta a cikin ƙasar in an cire tallafin man fetur.
An yi farar da Shugaban ne a wata hira ta musamman da jaridar Bloomberg ta intanet dake Amurka ta yi sannan ta wallafa a ranar Talata. Haka kuma BBC Hausa ta sake rubutawa da wallafa rahoton.
A cikin firar, Bloomberg ta tambayi Buhari me nene dalilin da ya sa ya ƙi amsa kiraye-kirayen da Asusun ba da lamuni na duniya IMF, da kuma Babban Bankin Duniya ke masa tsawon shekaru a kan ya janye tallafin man fetur, haka kuma canjin kuɗaɗen ƙasashen waje su zama na bai ɗaya?
Sai ya amsa inda ya ce, "har yanzu akwai ƙasashen yammacin duniya da ke bin tsarin biyan tallafin fetur".
Ya ƙara da cewa,
“To me ya sa za mu janye namu a yanzu?
“Abin da ƙasashen waje ke fama da shi shi ne sun fi mayar da hankali kan tsare-tsaren da aka yi a rubuce amma suna mantawa da tasirin haka ga al’ummominsu”.
A bara ne gwamnatin Shugaba Buhari ta so janye tallafin mai, saidai bayan fuskantar yadda abubuwan more rayuwa suka yi tsada tare da shawarwarin masu ruwa da tsaki a fannin sai aka ga ɗaukar matakin janye tallafi zai yi wahalar ɗauka.
Sai dai shugaban ya ce, ƙara samar da albarkatun man fetur a cikin ƙasar ta hanyar sababbin matatun mai da ake sa ran za su fara aiki nan gaba a wannan shekarar za su taimaka sosai.
Kan batun tsadar kuɗaɗen ƙasashen waje da mayar da farashinsu na bai ɗaya kuma shugaban Najeriyar ya ce hakan na faruwa ne sakamakon wasu abubuwa da ke faruwa a wajen kasar.
Ya ce,
“Idan aka ci gaba da samar da mai a cikin gida da tsare-tsaren samar da abinci, za a samu a daidaita farashin kuɗaɗen da mayar da su bai ɗaya a gwamnatance da kasuwar bayan fage".
Dubban ƴan Najeriya dai na kokawa kan yanayin tsadar farashi da hauhawar kayan masarufi, yanzu haka yayin rubuta wannan rahoto shinkafa ƴar waje ta kai Naira dubu biyu a garin Kano duk tiya ɗaya, itabkuwa shinkafar gida tana kai Naira dubu ɗaya da ɗari takwas inda ba ko ina ake samunta ba.
0 Comments