Talla

PANTAMI NADA ABUBUWA UKU DA ZAI SAMU AMSUWA A AREWA

 Daga: Musa Bello


An ɗauki Osinbajo Wanda pastor ne, wannan yasa mutanan kudu suka amshe shi ɗari bisa ɗari, har APC ta ci zaɓe. Don haka, yanzun ma idan aka ɗauki PANTAMI, a matsayin mataimakin TINUBU hakan zai ba APC damar samun cin zaɓe a Arewa, duba da shi ma malami ne dake da kwarjini da mabiya daga kowane ɓangare na yankin.

Na biyu, alaƙarsa Mai kyau tsakaninshi da Sheirk Dahiru Usman Bauchi kaɗai, itama zata Kara bashi damar sayar da a Arewa, domin lokutta da dama an ganshi gidan shehin malamin ya Kai mashi gaisuwar girmamawa. Hakanan Kuma an sha ganin diyan shehin malamin a ofishin Ministan amatsayinsu na yan gari daya da Kuma irin mutuntawa da Ministan keyima mahaifinsu, yasa suma suke Kai mashi ziyara har ofis nashi. 

Abu na Uku, PANTAMI ya tabbatar ma duniya ya goge akan fanninshi, ta yadda kullun samun numbobin girmamawa yake ko ta ina tare da yabo daga fadar gwamnatin tarayya, Wanda ko a cikin maganar shugaba Buhari ta ranar Demokaradiya sai da ya yabi Ministan sadarwar akan namijin kokarin da yakeyi a ma'aikatar tashi, bugu da Kari babu zargi na cin hanci da rashawa ko na sisin kwabo atare dashi, abinda yayi wuya yanzu.

Wato daukar PANTAMI a matsayin matemakin TINUBU tamkar lalata lissafin Jam'iyyar PDP ne a zabe Mai zuwa, domin ko ta bangaren malamai, dole su goyi bayan PANTAMI akan duk wani matemakin da wani Dan takarar shugaban kasa na wata jam'iyya zai dauko.

Kaucema yin hakan, tamkar fadawa ne tarkon PDP Wanda dama haka takeso, APC tayi kuskuren dauko Christer daga Arewa domin hakan ya bata damar yin wasan kura da APCn akakar zabe mai zuwa, domin ko shakka babu, idan APC tayi kuskuren dauko minority chister daga Arewa, to kafin karfe 12 na rana anyi zana'idar APCn

Don haka babu wata matsala akan yin Muslim- Muslim ticket kamar yadda hatta wasu daga cikin jiga jigan Kudu, cikinsu harda  pastor, suka fadi hakan da bakinsu. Ga abinda Orji Uzor Kalu da Femi Fani -kayode, Hope Uzodinma da dai sauransu suke cewa'babu wata matsala yin Muslim-Muslim ticket, domin gurinmu shine yin nasara, bawai faduwa zabe ba'

Post a Comment

0 Comments