Talla

Hatsaniya ta Kaure a Shalkwatar APC

 Daga: Bello Hamisu

ABUJA, NAJERIYA —Yayin hatsaniyar, wasu masu zanga-zanga sun yi ta sukar Shugaban jam'iyya.

Wasu matasa dai su isa a ofishin jam'iyya, rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa ta ƙara da cewa, matasan masu zanga-zangar sun riƙa yin waƙoƙi suna sukar shugaban jam'iyyar APC wato Abdullahi Adamu.

Kamar yadda jaridar ta ruwaito, ta ce, matasan sun fito daga Jihar Kogi, kuma sun isa shalkwatar ne lokacin da jam'iyyar ke wani taro.

Matasan sun nuna ɓacin ransu ne kan abin da suka kira da kwace tikitin takarar muƙamin ɗan majalisar wakilai da aka yi wa wani ɗantakararsu sai aka miƙa tikitin takarar ga wani mutumin na daban.

Jami'an tsaro sun kulle ƙofofin babban ofishin jam'iyyar ko lokacib da suka ji masu zanga-zangar na iƙirarin hana Abdullahi Adamu ficewa daga ginin.

Hatsaniyar ta tashi ne daidai lokacin da ake sa ran jin wanda za a ɗauka a matsayin mataimakin shugaban ƙasa. 

Ko ɗazu saida wani matashi mai nazarin al'umurran siyasa mai suna Musa Bello ya yi hasashen cewa da za  ɗauki Pantami lallai da kwalliya ta biya kuɗin sabulu.

Post a Comment

0 Comments