Talla

El-Rufai ya kori Shugaban NUT da malamai fiye da 2000

 Daga: Mohd Abdallah

KADUNA, NAJERIYA — Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da korar malamai sama 2,356, da suka gaza cin jarrabawar gwaji da aka yi masu.

Hukumar da ke kula da ilimi ta KADSUBEB ita ce ta sanar da matakin da aka ɗauka a ranar Lahadi, wanda ya shafi har da shugaban ƙungiyar malamai ta ƙasa Audu Amba.

Mai magana da yawun hukumar ta KADSUBEB wato Hauwa Mohammed ta ƙara da cewa, hukumar ta yi jarrabawar ne ga sama da malamai 30,000 a cikin watan Disamban 2021.

Ta ce kuma ce, sun kori malaman firamare 2,192 da suka haɗa da Shugaban ƙungiyar malamai ta ƙasa ta NUT, Audu Amba, saboda kin zana jarrabawar kwata-kwata.

Ta kuma ce, sun ƙori wasu malamai 165 daga cikin 27,662 saboda sun gaza samun makin da ya dace.

Arewa News ta ji ta bakin BBC Hausa inda take cewa,

"Ba a bukatar aikin malaman da suka samu maki kasa 40, saboda haka an kore su daga aiki".

Shugaban ƙungiyar malamai na jihar Kaduna Ibrahim Dalhatu ya yi watsi da jarrabawar, wadda ya ce ba a shirya ta kan ka'ida ba.

Ko a 2018 sai da gwamnati ta ƙori wasu malaman makaranta, lamarin da ya ja cece-kuce a cikin Jihar.

Post a Comment

0 Comments