Daga: Muhammad Bello
SOKOTO, NAJERIYA - A yammacin ranar Lahadi wasu ƴan bindiga suka saɗa wa wasu ƴan sa kai dake kusa da Zirin Daji.
Lamarin ya faru ne a wasu garuruwa na jihar Kebbi da ke kusa da iyaka da jihar Neja ɓarayin dajin sun yi masu kwanton ɓauna lokacin da ƴan sa kan suka bi su domin ƙwato dukiyar jama'ar da ƴan bindigar suka yi awon gaba da ita.
Dagacin garin Takita ya ce,
"Gaskiya sun masu kwanton ɓauna sun kashe wajen mutum 63. Lokacin da suka shigo da fari sun kwashi mutane da dabbobi ana ta ihun ga ɓarayi, to bayan sun wuce sai ƴan sa kan suka bi bayansu don ceto waɗanda suka kwasa".
Ya ƙara da cewa,
"To ashe sun yi wa ƴan sa kan kwanton ɓauna sun ɓuya a saman bishiyoyi, da isar ƴan sa kai wajen sai suka buɗe musu wuta suka kashe su sosai.
Ya ce sun tabbatar da adadin waɗanda suka mutun ne bayan kwaso gawarwakinsu don yin jana'iza.
"Ƴan sa kan da aka kashe ɗin sun fito ne daga garuruwa daban-daban ciki har da Takita da sauran wasu garuruwan huɗu.
Sai dai ya ce duk da cewa sun samu labarin su ma ɓarayin dajin an kashe wasu daga cikinsu, to ba su da tabbas akan yawan waɗanda aka kashen.
Lamarin dai ya faru ne ranar Lahadi da misalin karfe 8 zuwa 9 kuma an yi jana'izar tasu da misalin ƙarfe hudu na yamma.
Wani shugaban ƴan sa kai na garin Sanci, daya daga cikin garuruwan da lamarin ya shafa ya ce sai da suka ƙirga gawa 63 daga garuruwan Dabai da Magajiyya da Takita da kuma Rafin Zuru.
Shi ma kwamandan ƴan sa kai na ƙaramar hukumar Zuru ya ce bayan kwaso gawarwakin ne sai suka kai ofishin ƴan sanda inda kowane ɓangare suka je suka kwashi gawarwakin ƴan uwansu.
"Lamarin ya shafi yankin Zuru ne gaba ɗaya, an taɓa kowane ɓangare," in ji shi.
Ya ƙara da cewa sun samu tarnaƙi sosai wajen kwaso gawarwakin.
Har yanzu ana tattara bayanai don gano ainihin yawan mutanen da aka kashe.
Hare-haren ƴan bindiga da satar mutane don kudin fansa da satar dabbobi sun zama ruwan dare a arewa maso yammacin Najeriya.
Amma harin baya-bayan nan shi ne mafi muni da ya taɓa faruwa ga ƴan sa kan da ke faɗa da ƴan bindigar a yankin.
Garuruwan Katsina da Kaduna da Zamfara da Sokoto da Kebbi da Nija na daga cikin garuruwan dake fama da hare-haren ɓarayin daji masu satar mutane don karɓar kuɗin fansa.
0 Comments