Talla

Matar Abdulmalik Tanko Ta Bayyana Yadda Aka Kawo Mata Ajiyar Hanifa

Daga: Muhammad Abdallah


KANO, NAJERIYA - Matar Abdulmalik Tanko mutumin da ake zargi da kisan Hanifa a Kano, ta bayyana a gaban kotun shari'a Usman Na-Abba a karon farko a ranar Alhamis da safe haka kuma ta bayyana yadda mijinta ya kawo mata ajiyar Hanifa kafin daga bisani da matsa masa ya ɗauke ta.

Matar ta bayyana cewa, bata san lokacin da ya kashe Hanifa ya kuma binne gawarta ba. Da lauyoyi suka nuna mata hoton Hanifa a hoto ta shaida fuskar yarinyar.

Matar mai suna Jamila Muhammad Sani ta tsaya a gaban ƙuliya ne a matsayin mai bayar da shaida kan tuhumar da ake yi wa mijinta da sacewa tare da kashe Hanifa yarinyar ƴar shekara biyar a watan Janairu.

Jamila ta amsa tambayoyi daga lauya mai gabatar da ƙara, Barista Musa Lawan, inda ta yi wa kotu bayani kan abin da ta sani game da zargin ɗauke Hanifa, wacce ɗaliba ce a makarantar da ta zam mallakin mijinta Abdulmalik.

Ta ce ya kawo mata yarinya ta tambaye shi ina iyayenta sai ya ce mata mahaifiyar yarinyar ta sami aiki a Saudiyya, kuma ta tafi Abuja don ta cike wasu takardu na aikin.

Ta ci gaba da cewa,

"Amma har yamma na ga bai mayar da ita gida ba sai nake tambayarsa yaushe mahaifiyar yarinyar za ta dawo gida, kuma me ya sa har yanzu ba ta kira shi ba?"

Ya ce,

"Sai ya ce ba ta kira ba, daga baya sai ya ce sun yi magana da mahaifiyar yarinyar ta ce akwai layi ba za ta dawo ba a ranar ba,".

Ta ce, bayan kwana biyu sai ya sake ce wa mata mahaifiyar Hanifa ta taho amma wani uzuri ya tsayar da ita a hanya, daga baya da ta sake tambayarsa, sai ya ce ta daina tambayarsa.

Ta shaida wa kotu cewa yarinyar da ke jikin wani hoto da kotu ta yi wa laƙabi da hujja ta 5 lallai Hanifa Abubakar ce.

Sannan ta ce bayan kwana uku ta sake yi wa mijin nata Abdulmalik magana ya ce kuɗin mahaifiyar yarinyar ne ya ƙare tana Kaduna yanzu haka amma za ta dawo.

Saboda yadda ta matsa masa, sai ya faɗa mata cewar zai mayar da Hanifa wajen babarta.

Jamila ta ƙara da cewa a daren ranar na biyar ya sanar da ita zai mayar da Hanifa gida, a lokacin ta fara bacci, ya ce a ɗauko kayan makarantarta a saka mata.

Duk da ce masa da ta yi dare ya yi a lokacin 11 na dare, amma haka ya tafi kai ta wajen iyayenta.

Ta ce,

"Lokacin da ya dawo na fara bacci, na kuma tambaye shi cewar ya mayar da yarinyar gida? Sai ya ce 'e'.

Ta ce,

"Bayan ƴan kwanaki sai na ga wata farar waya a hannunsa, sai na tambaye shi inda ya same ta sai ya ce min ta wani Hashimu Isyaku ce ya ba shi ya saka masa caji," 

Jamila ta bayyana cewa tun daga lokacin bata ƙara jin labarin Hanifa har sai ta DSS suka zo yin bincike gidansu. Ba ta samu labarin ɓacewar Hanifa da mutuwarta ba kuma gano gawarta ba ko wajen makwabtanta.

Jamila dai ta amsa tambayoyi kafin daga bisani a ɗage sauraron ƙarar.


Ana zargin cewa Abdulmalik me ya sace Hanifa tare da bata guba ta sha sannan ya binne gawarta.

Post a Comment

4 Comments

  1. Turkashi! Allah dai ya baiwa wannan Alkali damar yanke hukuncin gaskiya amin.

    ReplyDelete
  2. Wai ga gaskiya na barobaro amma sai daga kara akayi hmmm at d end of dis stupidity judgment dey r postpone they live dis man and he doesn't no anything about it. Yaza'ayi Nigeria tajaru tinda baza'ayi adalci akan lkc ba

    ReplyDelete
    Replies
    1. Don dai an ce shari'a shabanin hankali, amma ina tsoro a saki wannan mutumi ba tare da yanke mana hukunci ba, this is nigeria.

      Delete
Emoji
(y)
:)
:(
hihi
:-)
:D
=D
:-d
;(
;-(
@-)
:P
:o
:>)
(o)
:p
(p)
:-s
(m)
8-)
:-t
:-b
b-(
:-#
=p~
x-)
(k)