Kungiyar Marubutan Jihar Katsina (KMK)
An karanta wannan labari tare da yin bitarsa wajen Reading Session da Kungiyar Marubutan Jihar Katsina KMK ta gudanar a ranar 12 ga watan Febrairu, shekara ta 2022.
***
Farkon Labarin
Sannu a hankali Hasiya ke
hawa matakalar benayen dake ɓangaren ofisoshin Malamai, da za ka kalleta a
lokacin, sai ka yi zaton jikin ta ba na jini da tsoka bane saboda tsabar
karairayar da take yi.
Kai tsaye ofishi mai lamba
sha takwas ta nufa, tun daga nesa ta ƙara canza takun tafiyarta, ba don komai
ba, sai don kada ta samu matsala su haɗe da Malan Ɗan Furofesa a waje ta ƙi
samun abinda ta zo nema cikin sauƙi. Da zuwan ta dai-dai ƙofar ofishin, sai ta
saka hannu ta murɗa mabuɗin ƙofar tare da turawa, sannan ta shiga ciki tare da
yin sallama da wata murya mai saurin jan hankalin ɗa namiji.
Ƙanshin turaren ta, da
sautin muryar ta suka dakar masa zuciya, cikin sauri ya ɗauko da kan sa domin
ganin ko wace ce. Hasiya ya gani cikin wata rikitacciyar shiga mai saurin tayar
da zaune tsaye, yayin da bakin ta ke tauna cingam gwanin ban sha'awa da
burgewa, wannan daliline yasa gaba ɗaya ta tafi da imanin sa, domin bai san
lokacin da ya shagala ga kallon duk wata kusurwa ta jikin ta da ta bayyana ba.
Lokacin da Hasiya ta lura da
irin kallon da Malam Ɗan Furofesa ke yi mata, sai ta sake kashe murya a karo na
biyu sannan tace, "Malan ina kwana!"
Ajiyar zuciya yayi, tare da
ajiye takardun dake hannun sa, sannan yace, "Lafiya lau Hasiya, Me ke tafe
dake waje na da wannan sabon salon da ban saba ganin ki da shi ba?"
Murmushi Hasiya tayi, sannan
ta zauna bisa doguwar kujerar dake cikin ofishin tana mai ɗora ƙafa ɗaya bisa ɗaya,
sannan tace da Malan Ɗan Furofesa, "Malan jiya na je an duba man result ɗina
a difatment, ko ina na ci amma ban ci kwas ɗin ka ba."
Gyara zama yayi ya cigaba da
zuba mata ido, sannan yace da ita, "Allah ne ya ƙaddara maki haka, sai
kiyi hakuri".
Hasiya na jin haka sai ta taɓe
baki, sannan tace da shi a cikin muryar shagwaɓa, "Haba Malam! Dan Allah
ka taimake ni mana, wallahi ba ni so ƙawaye na su fahimci na fadi kwas ɗin nan,
a matsayina na babbar yarinya za ai mani dariya."
Murmushi ɗan Furofesa yayi
da jin ta fadi haka, sai yace da ita, "Hasiya ai ba ki shirya cin kwas ɗin
ba tun farko, da kin shirya da kin bi hanya ɗaya da waɗanda su ka ci kwas ɗin".
Hasiya na jin haka, sai ta
ajiye jakar dake hannun ta, sannan ta mike tsaye tare juyawa a gaban malam Ɗan
Furofesa, sannan tace, "Malan ka dube ni sama da ƙasa, ka san na ci sunan
babbar yarinya, ban damu da duk abinda zai faru ya faru ba muddin za ka gyara
man sakamako na ya koma mai kyau."
Murmushi yayi tare da riƙe
baki, domin bai yi zaton zata fadi haka ba, amma sai yace da ita, "Hasiya
koma meye fa kika ce !"
Girgiza kai Hasiya tayi tare
da cewa, "Ƙwarai da gaske malam, ai ranar cikar buri rai ba a bakin komai
yake ba!"
Jin haka yasa ya miƙe tsaye
tare da zagayowa gaban teburin sa ya zauna, ya na mai cigaba da kallon ta,
sannan ya ce, "Je kulle ƙofar shigowa da makulli ki dawo na ga idan za ki
iya."
Cikin tafiyar ta mai tattare da jan hankali
ta nufi ƙofar ta rufe, sannan ta dawo kusa da shi ta tsaya ta na mai cigaba da
yi masa murmushi.
Ganin haka yasa malan Ɗan
Furofesa ya ce da ita, "Kawo kunnen ki na faɗa ma ki wani abu da zai maki
amfani muddin ki na so ki ci kwas ɗin."
Ba tare da wata gardama ba
ta duƙo da kanta dai dai bakin sa, sanan yace da ita, "A dage shekara mai
zuwa ayi karatu sosai domin samun damar cin kwas ɗin, amma ni ba ɗan iska bane kamar
yadda kika yi tunani."
Jiki a sanyaya ta janye
kunnen ta daga saitin bakin sa, har ta duɗi baki zata yi magana, sai ya ɗaga
mata hannu, sannan yace, "Kada ki ce komai Hasiya, ki godewa Allah na taɓa
son ki da Aure a cikin zuciyata, amma ba dan haka ba, wlh da sai na kai ki gaba
an kore ki, saboda haka tun kafin na canza shawara ki fice mani daga
ofis!"
Kamar Kazar da ƙwai ya fashe
mawa a cikin ciki, haka Hasiya ta nufi hanyar fita daga cikin ofishin zuciyar
ta cike da ƙunci da ɓacin rai, zuwa can sai wani ɓangare na zuciyar ta ya ce da
ita, "Ke fa babbar yarinya ce, tunda ki na da kyawun da duk wani makwaɗaicin
namiji zai yi mararin ki, kawai ki je gurin na sama da shi, ƙila ki dace burin
ki ya cika".
Da wannan zancen zuci Hasiya
tayi amfani, kai tsaye kuma ta nufi ofishin shugaban difatment ɗin su, bisa
sa'a ta taradda ashe Kazagi ne, baya ganin banza bai ci ba.
A cikin abinda bai wuce awa ɗaya
da rabi ba ta gamsar da shi, shi kuma ya gamsar da ita ta hanyar sawa a goge
mata faɗuwa, sannan ta nufi gurin kwanan ɗaliban su na mata zuciya cike da
farin ciki, har tana faɗawa zuciyar ta cewa, "Ai sai wani mutuncin ya zube
ake ɗaukar wani!"
****
A haka Hasiya babbar yarinya
ta kasance, muddin ta samu faduwa a wani kwas, to jikin ta shine abin bayarwa
ga makwaɗaitan Malamai domin a gyara mata, hakan yasa girman kanta ya ƙaru,
abokan karatun ta har kirari suke mata da cewa, "Babbar yarinya a wanka,
babbar yarinya a GP!"
Lokacin da sakamakon
jarabawar shekarar ƙarshe ya fito, sai Hasiya ta ganta da tarin faɗuwa, wanda a
tunanin ta tuni malaman da ta gyaramawa sun daɗe da gyara mata su.
Cikin tashin hankali ta bi
Malaman ta sanar da su, amma daga ba ta haƙuri babu abinda suke iya yi mata,
wannan daliline yasa ba ta san lokacin da ta yanke jiki ta faɗi ƙasa sumammiya
ba!
Lokacin da aka kaita
Asibiti, sai likitoci suka tabbatar da tana ɗauke da cutar dake karya garkuwar
jikin dan adam, watau ƙanjamau.
Baƙin ciki a wajen Babbar Yarinya ba a
magana, ta na ji ta na gani ta hakura da makarantar ta koma gida ta zauna, tana
mai nadamar biyewa dokin zuciya.
0 Comments