Talla

Kwalliya Ta Biya Kuɗin Sabulu: Kakaki Unique Awards

 Daga: Bello Hamisu Ida


KATSINA, NAJERIYA - Kakaki Unique Awards: Kwalliya Ta Biya Kuɗin Sabulu

Wata ƙungiya mai zaman kanta wadda aka yi wa rigista da hukumar rigista da Ƙasa, ƙungiyar ɗaya ce tamkar da dubu ta zaƙulo wasu jajirtattun mutane tare da miƙa masu kambun girmamawa a wani taro data gabatar a Jihar Katsina. Ba wannan karon ne ta gabatar da taron ta na farko ba, ta na gudanar da taron duk shekara, kuma wannan shi ne taronta karo na shidda inda ta buɗe asusun taimakon matasa masu fikira da hikima da azanci waɗanda take ɗaukar nauyin karatunsu da sauran hidimominsu na rayuwar yau da kullum. A wajen taron kafin da miƙa kambun girmamawar, ta gabatar da wasu yara matasa masu hikima waɗanda aka ɗauki nauyin karatunsu da lafiyarsu da tufafinsu tun daga karatunsu na matakin firamare da sakandare da makarantar gaba da firamare har zuwa samun aikinsu.

Kakaki Unique Award 2022 ta zo da sabon salon girmama al’ummar Arewacin Najeriya dama sauran mutane da ke da fikira dake ciki da wajen ƙasar. ƙungiyar ta bayar da lambar yabo, haka kuma ta karrama waɗannan yara, matasa masu fikira, basu kaɗai ba har da masu hannu da shuni da mashahuran mutane da suka halarci taron a karo na shida da yammacin ranar Lahadi a cikin Jihar Katsina.

Babban jami’in gudanarwa na kungiyar wanda Arewa News ta yi wa laƙabi da ‘Mai Maƙogoron Zinari’ jajirtaccen matashi wanda aka fi sani da sunan Kabiru Sa’idu Bahaushe, ya ce an ƙirƙiro wannan karramawar ce don zaburar da al’umma wajen ƙara kaimi a fannonin da suka yi shuhura.

A wajen taron akwai mabambanta mutane, tun daga ‘yan kasuwa, masu shirya fina-finai, lackarori, yan siyasa, marubuta da sauran mutane da ke da fikira da azanci da hikima da kwarewa a fannonin rayuwa daban-daban. Waɗannan matasa ‘yan bana bakwai waɗanda suka kasance ɗalibai sun nuna kwarewarsu a fannonin rayuwa inda suka gabatar da wasu ƙawatattun zane-zane da hotuna da rubuce-rubuce da aka yi a saman takarda da wani irin salo na musamman, haka kuma sun bayyana yadda suke jajircewa a makarantunsu don nemarwa kansu ingantacciyar rayuwa.

An gabatar da kyaututtuka ga marayun don zaburar da su yayin da suke ci gaba da fafutukar neman tsira a cikin rayuwarsu. 

Mai maƙogoron Zinari ya yi ƙarin bayani da cewa, Kakaki bata neman kuɗi da kowa illa iyaka tana nemo jajirtattun mutane da suka yi shuhura sannan kuma tana zaƙulowa tare da taimakon rayuwar yara matasa waɗanda suke da wata fikira ɓoyayya don su samu bayyana fikirarsu sannan kuma al’umma ta amfana da irin baiwar da Allah ya yi masu.

Bayan an buɗe asusun taimakon yaran, inda aka samu gudummuwa daga mabambanta mutane, an kuma bayar da kambun karramawa ga waɗannan shahararrun mutane:

1. Dr. Sani Abdu Fari

2.Abdulbaki Jari

3.Jamilu Yahaya Kankara

4. Faisal Suleiman

5. Alh. A/Wahab Shagumba

6. Alh. Muntari Bawa

7. Tukur Tingili

8. Kabir Moto

9. Bello Hamisu Ida

10. Alh. Muhammad Tukur Ibrahim Safana

11. Abdul Amart Mai Kwashewa

12. Hon. Faruk Lawal Ayuba

A yayin bikin, babban jami’in kaddamar da shirin Film Abdu Amart ya sanar da bayar da tallafin naira milyan 1,000,000, haka kuma, Alhaji Abdulaziz Mai Turaka, ya bayar da naira miliyan biyu (N2,000,000). Haka kuma, Kwamishinan kasafi da tsare-tsare na tattalin arzikin Jihar Katsina Faruk Jobe da Muhammad Usman Sarki shugaban kamfanin Al Dusar Limited sun sadaukar da albashinsu na wata ɗaya, yayin da ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kankia, Kusada da Ingawa, Abubakar Kusada ya ba da Naira 300,000, haka kuma mai ba gwamna Masari shawara ta musamman kan ci gaban ‘Ya’ya mata wato Amina Dauda Mani ta bayar da Naira 200,000.

Daga ƙarshe an yi hotuna cikin annashuwa da farin ciki da saka albarka kan waɗanda suka shirya wannan taro mai albarka.



Post a Comment

0 Comments