Daga: Bello Hamisu Ida
KATSINA, NAJERIYA — A ranar 6 ga Maris, 2022 da misalin karfe 1930 na safe, an samu kiran gaggawa
cewa, an ga ‘yan ta’adda masu yawa, ɗauke da bindigogi ƙirar AK 47 a kan babura, a wata mummunar manufa ta zuwa ƙauyen
Barawa, dake ƙaramar hukumar Batagarawa ta Jihar. An tattaro tawagar ‘yan sanda da sojoji zuwa yankin, inda suka yi
artabu da ‘yan bindigar sannan rundunar jami’an ta samun nasarar fatattakar su.
SP Gambo
Isah, ANIPR, Jami'in
Hukuncin Jama'a (PPRO), ya yi ƙarin
bayani a wani dandali na sada zumunta na Popular Hausa News, inda ya ce,
Dabarun da jami’an
tsaro suka nuna ya sa 'yan
ta'addan suka tsorata sannan suka ari takalman kare suka arci cikin daji. An gano babura na ‘yan bindigar guda biyar. Daga bisani, DPO na Batagarawa ya kwato wasu babura na ‘yan fashin wanda suka
ruga suka bar su a cikin dajin Barawa. Ko
da yake ‘yan bindiga da dama sun tsere da harbin bindiga a jikinsu. An umurci jama'ar yankin da su kai rahoto ga jami'an tsaro mafi kusa in suka ga
wani da mummunan rauni.
Kwamishinan
‘yan sandan Jihar Katsina, CP Idrisu Dauda Dabban, PSC, FDC, ya ga ƙoƙarin jami’an na daƙile ‘yan ta’adda. Ya kuma buƙaci jama’a da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro haɗin kai wajen yaƙi da ta’addanci a jihar.
Garuruwan Katsina da Kaduna da
Zamfara da Sokoto da Kebbi da Nija na ɗaya daga cikin garuruwan dake fama da
hare-haren ɓarayin daji masu satar
mutane don karɓar kuɗin fansa.
1 Comments
Allah shi tsare mu
ReplyDelete