Muhammad Bello (Arewa News)
ABUJA, Najeriya — farkon wannan wata wato watan
maris, daidai lokacin da ƙasashen duniya suke kara saka ido da yin Allah wadai
ga yaƙin dake faruwa a ƙasar Ukraine tsakanin ƙasar da Rasha, duk da yake ba ƙasar
ce kawai ke cikin matsalar tashe-tashen hankulla ba, akwai wasu ƙasashe da ke
fama da faɗan cikin gida, wasu kuma ƙasashen na fama da faɗa tsakanin
makwabciyar ƙasar.
A Najeriya, a Arewacin ƙasar, musamman a
Jihohin Katsina da Kaduna da Zamfara da Sokoto da Kebbi da Nija dama wasu
jihohi dake Arewacin ƙasar na fama da tashe-tashen hankula, da ɓarayin shanu da
masu satar mutane don ƙarɓar kuɗin fansa da kuma sane da sata da fashi da
kwace.
Ko a watannin da suka gabata, an kama wani
Mutum wanda ya sace ɗalibarsa sannan ya kashe ta bayan ya bata guba ta sha, ya
kuma nemi kuɗin fansa wajen iyayenta. Labarin Hanifa da malaminta ya ja hanalin
duniya sosai, al’amarin da ya faru a garin Kano. Ba Hanifa kaɗai ta shiga irin
wannan mummunar ƙaddarar ba, akwai yara da yawa da aka sace wasu aka kashe
sannan aka salwantar da gawarwakinsu.
A Jihar Katsina, duk da yake ana ganin cewa an
samu sauƙi da ingantar tsaro amma dai ana samun ɗaiɗaikun hare-hare da
sace-sace. Ko a cikin satin nan sai da rundunar yansandan Jihar Katsina ta samu
nasarar kama wasu gungun ɓarayi da suka addabi birnin da makwabtan birnin da
sace-sace. Ba wannan gungun kaɗai yansanda suka kama ba, sun sake kama wani
mutum mai suna Sabi’u Duna da ya kware wurin sayen kayan sata a hannun ɓarayi
da ke sace-sace a cikin birnin. Kakakin rundunar SP Gambo Isah ne ya gabatar da
wanda ake zargi a gaban manema labarai.
A jihar
Kaduna shekaranjiya ne wasu da ake zargi masu tayar da ƙayar baya ne suka dasa
wani bom a wani hotal dake ƙaramar hukumar Igabi. Tashar Channels TƁ ta ce,
fashewar ta afku ne da misalin karfe 11 na daren Lahadi, kuma ta shafi wasu
sassan ginin da ke ɗauke da wata cibiyar kallon kwallon kafa.
An yi sa'a ba a sami asarar rai ba saboda babu
kowa a cikin ginin lokacin da bam ɗin ya tashi.
Jami’an tsaro karkashin jagorancin kwamishinan
tsaron cikin gida da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan da kwamandan Garrison
na shiyya ta 1 ta Mechanized na sojojin Najeriya Birgediya Janar Tamuno Opuene
sun ziyarci wurin da fashewar ta afku a ranar Litinin.
Akalla mutane tara ne suka mutu, wasu da dama
kuma suka rasa matsugunansu, a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a
daren Lahadi a wasu kauyukan karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.
Wani ɗan fashi da makami mai suna Adamu Aleru a
dajin Tsafe yafi ƙaddamar da ayyukan ta’addanci ga al’ummomin da ke ƙarƙashin ƙaramar
hukumar Tsafe dake Jihar Zamfara da ƙaramar hukumar Faskari dake Jihar Katsina.
Wani mazaunin garin Tsafe mai suna Salisu Sabo
ya shaida wa Premium Times cewa ƙauyukan da aka kai harin a daren Lahadi sun haɗa
da Magazawa, Kajera, Unguwar Dan Halima, Unguwar Rogo, Unguwar Ango, Kurar Mota
da Kauyen Kane duk a ƙarƙashin gundumar Bilbis.
Ya ce,
“Sun gudanar da hare-hare, amma mafi muni shi ne
wanda suka gudanar a ƙauyen Magazawa inda aka kashe mutane bakwai. An gano
gawarwakin ne da safiyar ranar Litinin. A wasu ƙauyukan dai ba mu ji an yi wani
kashe-kashe ba, amma galibin mazauna yankin sun gudu zuwa garin Tsafe. Na ga
mata sama da 50 sun shigo Tsafe a safiyar yau,”
A jihar Sokoto, a gabashin jihar ya jima yana
fama da waɗannan matsalolin, inda a wasu lokuta ko an ga alamun sauƙi sai
matsalar ta koma sabuwa.
Al'ummomi da ke ƙaramar hukumar Illela garin da
a Najeriya ke makwabtaka da Jamhuriyar Nijar, suna fuskantar ƙaruwar matsalolin
tsaro, duk safiya sai an samu rahoton kai hari ko an kashewa ko kuma ace an
sace mutane.
Kauyen Danbar Dikko ƙauye ne na Fulani, a ƙarshen
makon da ya gabata jama'ar garin sun tsinci kansu cikin tashin hankali
sanadiyar wani hari da aka kai garin wanda suke zargin Hausawa ne suka kai
musu.
VOA Hausa ta ruwato Mai garin na Dambar Dikko na
cewa; abin ya zo masu da mamaki domin suna zaman lafiya da Hausawan amma
kwatsam sai ga wannan farmakin an kai musu.
VOA Hausa ta yi ƙoƙari don jin ƙarin bayani a
bakin rundunar ansandan Najeriya, amma bata samu dama ba har zuwa rubuta wannan
rahoto.
Garuruwan Katsina da Kaduna da Zamfara da
Sokoto da Kebbi da Nija na daga cikin garuruwan da ke fama da matsalar tsaro da
ɓarayin shanu da masu satar mutane don karɓar kuɗin fansa, kodayake hukumomi da
jami’an tsaro na yin iyakacin ƙoƙarinsu don kawo zaman lafiya ƙasar Najeriya,
saidai har yanzu yan ƙasar na barci da ido ɗaya. (Arewa News) www.arewanews.org.ng
ko www.arewa.com.ng
Shugaba Buhari Ya Yabawa Gwamnan Jihar Nasarawa Bisa Ƙoƙarin Samar Da Ababen More Rayuwa
Shin da Gaske Ne Hushpuppi Ya Mutu?
Babu Wata Ƙaramar Hukuma A Najeriya Da Ke Ƙarƙashin Ikon 'Yan Ta'adda - CDS
0 Comments