Daga: Muhamamad Abdallah
KADUNA, NAJERIYA — Gwamnatin jihar Kaduna ta gargaɗi mutanen jihar su yi taka-tsantsan wajen
yin hidimominsu na yau da kullum domin ana fargabar masu tayar da ƙayar baya sun
dasa nakiyoyi a sassan jihar. Satin da ya gabata ne wani bam ya fashe a wani
hotel dake ƙaramar hukumar Kabala dake Kudu.
A ranar 27 ga watan Fubrariru shekara ta 2022 ne wani bam ya
fashe a wajen. Gwamnatin Jihar ta nusar da al’ummar jihar ne bayan fashewar
wannan nakiya wanda ake hasashen wasu ne suka dasa ta.
Kwamishinan tsaro da lamuran cikin gida na jihar wato Samuel
Aruwan ne ya bayyana wannan ankararwa a sanarwar da ya fitar.
Sanarwar ta ƙara da cewa, an shuka nakiyoyin a wajen da
mutane ke taruwa kamar makarantu, asibitoci, masalatai, coci-coci, hotel-hotel,
gidajen barasa, filayen shakatawa, gidajen abinci, tashoshin mota.
Gwamnatin ta nemi masu fasa dutse su yi takatsantsan a filayen
aikinsu don gujewa barin nakiyoyin su faɗa hannun ɓata gari.
Bayan wannan, sanarwar ta buƙaci mutane su kira jami’ai a duk
inda suka ga wani abu da suke zargi ko suka ga wani abu da ba su yarda da shi
ba koma suka ga wani ko wasu mutane da take-takensu bai kwanta rai ba ko suke
aikata wani abun rashin gaskiya, ko su kira lambobin jami’an tsaro. (Arewa News) www.arewanews.org.ng ko www.arewa.com.ng
Wasu Labarai
Shugaba Buhari Ya Yabawa Gwamnan Jihar Nasarawa Bisa Ƙoƙarin Samar Da Ababen More Rayuwa
Shin da Gaske Ne Hushpuppi Ya Mutu?
Babu Wata Ƙaramar Hukuma A Najeriya Da Ke Ƙarƙashin Ikon 'Yan Ta'adda - CDS
0 Comments