Daga: Muhammad Abdallah
KATSINA,
NAJERIYA —
Duk da tsananin wahalar man fetur da ake yi a faɗin
ƙasar Najeriya, gobara ta kama a
wani gidan mai dake garin ‘Yantumaki garin dake cikin ƙaramar hukumar Danmusa take yankin Funtua Zone,
gidan man fetur ɗin mai suna SUKAMOS ya kama da
wuta ne a ranar Talata.
Wasu
ganau sun shaida cewa wutar ta kama motoci biyu masu ɗauke da man fetur da aka ajiye a cikin gidan man
inda mutane suka jera ababen hawansu don su sha mai.
Al’ummar
garin ‘Yantumaki dai sun yi ta ƙoƙari
wajen kashe wannan gobara kafin jami’an kashe gobara su isa wajen.
Wani
na kusa da walikin Arewa News ya shaida masa cewa, har zuwa lokacin da ya bar
inda gobarar ta kama babu wasu hukumomi da suka isa wajen, saidai an kira su
kuma ana sa ran zuwansu a kowane lokaci.
Tsawon wata ɗaya kenan da ‘yan
Najeriya ke ta fama da ƙarancin man fetur, wanda ya taimaka sosai wajen hauhawar farashin
kayan masarufi da sauran abubuwan more rayuwa.
A wasu jahohin
farashin man fetur ya haura naira ɗari uku a duk lita ɗaya. Wasu gidajen man kuwa su kan saida leta a kan naira ɗari biyu da talatin
ko da arba’in, ya yinda galan ɗin mai yake kamawa dubu ɗaya da ɗari shidda ko ma abinda ya fi haka a kasuwar bayan fage.
Ƙasar ana shan wahala sosai kafin a samu a sha mai a gidajen mai, bayan kuma an zo sha a kan samu man ya yi tsada sosai inda ya haura naira dari da sittin da biyar wato farashin da gwamnati da saka a saida man fetur. (Arewa News) www.arewanews.org.ng ko www.arewa.com.ng
Wasu Labarai
Shugaba Buhari Ya Yabawa Gwamnan Jihar Nasarawa Bisa Ƙoƙarin Samar Da Ababen More Rayuwa
Shin da Gaske Ne Hushpuppi Ya Mutu?
Babu Wata Ƙaramar Hukuma A Najeriya Da Ke Ƙarƙashin Ikon 'Yan Ta'adda - CDS
0 Comments