Daga: Hauwa'u Bello
Wasu
'yan fashi ne suka shigo wani gida sai suka iske
mai gidan, suka tambaye shi kuɗi,
ya
ce; babu kuɗi, kawai
sai ɓarayin suka gyara bindigar su za su
harbi mai gidan,
Sai matar
sa tayi wuf ta tsaya a gaban sa,
Sai
suka harbe ta.
Bayan
ɓarayin sun tafi aka kai ta
asibiti, ta yi jinyar wata
10 a asibiti, sannan ta samu
lafiya, aka sallamo ta. Tana zuwan ta gida, sai
ta tarar da wata kyakykyawar budurwa a gidan, ta tambaye ta tace,
“Ke
kuma daga ina?”
Sai
ta ce, “Ni ce amaryai gidan, ai yau wata na tara 9
da ‘yan kwanaki”.
“Ke
kuma wace ce ke?” ta tambayi uwargida.
Idan
ke ce ya zaki yi ?
0 Comments