Daga: Hauwa’u Bello
ABUJA, NAJERIYA — Wata
yarinya ta ɓace a Jihar Lagos bayan
ta shiga motar BRT wadda ta yi farin jini da jigilar al’umma a faɗin jihar. Ƴan ƙasar Najeriya suna ta mayar da ba’asin bakinsu tare da nuna kaɗuwa
kan sace yarinyar wadda daga bisani aka kashe matashiya a jihar Lagos da ke
kudu maso yammacin ƙasar.
Ana tuhumar ɗaya daga cikin direbobin motar mallakar gwamnati Jihar Legas wadda
aka fi sani da sunan BRT wato Bus Rapid Transit a turance, saidai an kama shi
direban, inda ake tuhumarsa da sace yarinyar.
Matashiyar tana da shekara
ashirin da biyu kuma ta bace ne tun karshen watan Fabrairu bayan da ta shiga
motar ta BRT mai farin jini.
Labarin abin da ya faru ga matar
ya tayar da hankulan jama'a har ta kai ga an fara wani gangami a shafukan sada
zumunta, inda ake neman adalci ga matar: an buɗe wani batu da ake tattaunawa mai take Justice for Bamise a Tiwita.
Gwamnatin jihar Legas ta yi alƙawarin ɗaukar matakin shari'a kan duk wanda aka samu yana da hannu kan
sacewa tare da kashe matar.
0 Comments