Talla

An Tashi Baram-baram A Tattaunawar Kan ASUU Tsakanin Ministan Ilimi Da Shugaban Ɗalibai

Daga: Hauwa'u Bello


ABUJA, NAJERIYA - An dai yi tattaunawar ne tsakanin ministan ilimi da shugabannin ɗaliban Najeriya a babban birnin Abuja, a yayin tattaunawar an tashi baran-baran tsakanin mutanen biyu wato ministan ilimi Adamu Adamu da shugabannin ɗalibai a Najeriya, tattaunawar dai an yi tane kan batun yajin aikin ƙungiyar malaman jami’a ta ASUU.

Bayan shugaban ɗalibai dake jagorantar dubban ɗalibai a faɗin ƙasar ya gabatar da ƙorafinsu sai Ministan ilimi da fice daga zauren tattaunawar.

A lokacin da yake jawabi, shugaban ƙungiyar ɗaliban na Najeriya wato Sunday Ashefon ya faɗa wa ministan cewa shi ministan ya kai ɗansa ƙasar waje don ya yi karatunsa ba tare da wata tangarɗar yajin aiki ba.

An wani bidiyo da aka yaɗa a tiwita, an nuna yadda shugaban yake jawabi da kuma yadda ministan ya bayar da amsa sannan kuma ya yi ficewarsa daga zauren tattaunawar.

Cikin kakkausar muryar shugaban ɗaliban ya ce,

“Mun gani a kafofin sada zumunta, kana biki ɗanka ya kammala karatu a ƙasar waje."

Ya ƙara da cewa,

“Iyayenmu ba su da kuɗin kai mu ƙasahen waje, muna son a ware kuɗi domin ci gaban ilimi a ƙasar nan.”

Ya kuma ce,

“Mai girma minista muna son mu koma makaranta” 

Ministan bai yi wani dogon bayani ba sai kawai ya yi ficewarsa daga ɗakin taron.

Ƙungiyar malaman jami'a a Najeriya da aka fi sani da sunan Academic Staff Union of Universities wato (ASUU) dai ta faɗi matsayarta game da tafiya yajin aiki.

Bayan kamala wata tattauanwarsu da suke yi, sun faɗi abinda suka tattauna a kai da kuma matsayar da suka cimmawa.

Ƙungiyar malaman jami'a a Najeriya da aka fi sani da sunan Academic Staff Union of Universities wato (ASUU) ta faɗi matsayarta a yau game da tafiya yajin aiki. Ana sa ran jin cikakken bayani daga ƙungiyar a kan ranar da zata fara yajin aikin wanda ta kira yajin aikin gargaɗi na wata ɗaya.

(Arewa News) www.arewanews.org.ng ko www.arewa.com.ng

Post a Comment

0 Comments