Talla

Laifi Tudu Ne: Gwamnatin Kano Ta Sallami Wasu Ma’aikata Da Take Zargin Sun Saida Wasu Filaye

Daga: Hauwa'u Bello

KANO, NAJERIYA - Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da sallamar wasu ma’aikata waɗanda take  zarginsu da laifin yin takardun jabu tare da sayar da wasu filaye waɗanda suka zama ƙaddara kuma mallakin hukumar da suke aiki. Ma'aikatan dai suna aiki ƙarƙarshin Hukumar Ƙasa da Safiyo.

Korar ma'aikatan na ɗauke cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Kano wato Malam Muhammad Garba ya fitar a ranar Alhamis.

A cikin sanarwar an ce, kwamitin bincike da aka kafa wa ma’aikatan ya gano cewa ma’aikatan sun yi amfani da takardun bogi sannan suka sayar da filayen gwamnati wanda hakan ya saɓa dokar aiki ta gwamnatin Jihar a dokar aiki mai lamba ta 04406.

Ma’aikatan da abin ya shafa sun haɗa da: Abdulmuminu Usman Magami, mai matakin albashi na 6 da Abdullahi Nuhu Idris mai matakin albashi na 10 da kuma Audu Abba Aliyu mai matakin albashi na 05.

Sauran wanda abin ya shafa ya haɗar da Baba Audu mai matakin albashi na 13.

Daga karshe sanarwar ta ja hankalin ma’aikatan gwamnatin jihar da su kasance masu bin doka da oda.

Ba a wannan Jihar kaɗai band ma'aikata ke almundahana da cikin ma'aika da kayan kwamnati ko kuma wasu da suka faɗo don su gudanar da wani aiki.

Post a Comment

0 Comments