Daga: Muhammad Abdallah
ABUJA, NAJERIYA — Maraharan
boko haram sun kai wasu sabbin hare-hare a garin Gamboru-Ngala wanda ke da
iyaka da ƙasar Najeriya da Kamaru, mazauna garin sun tabbatar da cewa mayaƙan
sun kai hare-haren ne a daren lahadi wanda ya ɗauki su tsawon dare har zuwa
safiyar litinin sannan suka fita daga garin.
Mutanen garin sun ce, sun fara
jin harbe-harbe da tsakar dare sannan kuma suka sake jin ƙarar fashewar wani
abu mai kama da nakiya. Wani ganau ya shaida cewa,
“harin ya faru ne da daddaren
lahadi wajen ƙarshe sha biyu da rabi, mun ji ƙarar harbin bindiga ta ko ina,
mun yi ƙara a wajen makarantar firamare da tsakiyar gari”
Ganau ɗin ya ƙara da cewa,
“Bayan harbe-harben da mayaƙan
boko haram suka yi, sun kuma harba rokoki cikin makarantar inda sojoji suka yi
sansaninsu”
Harin ya rutsa da mutane da dama
ciki har da wani dattijo wanda ya rasa ransa bayan rokar ta faɗa cikin gidansa,
kodayake sauran iyalansa sun tsira da ransu. Wasu da harin ya rutsa da su an
tafi da su asibiti domin ayi masu magani.
A cikin makon jiya ne gwamnan
Jihar Borno Babagana Umara Zulum ya kai wata ziyara ta musamman garin na
Gamboru, inda ya ƙaddamar da wasu ayyuka, ciki har da buɗe hanyar da ta taso
daga garin zuwa Maiduguri ta garin Dikwa. Haka kuma, Gwamnan ya kuma kaddamar
da wani shiri na inganta tsaro, wanda a ƙarƙashinsa aka samar da ƙarin jami'an
tsaro.
Duk da waɗannan ayyuka da gwamna
ya buɗe bai hana mayaƙan shiga garin tare da tayar da zaune tsaye ba. Mutanen garin
sun bayyana yadda suka samu karyewar zuciya inda suke jin babu daɗi game da
wanann hari.
Saidai bayan wayewar gari, mafi
yawan mutanen garin suna zauna a cikin garinsu suna jiran tsammanin abinda zai
faru. Koda safiyar litinin saida ɗaliban makaranta suka yi yunƙurin shiga
makarantar don ɗaukar darussansu, saidai ba’a basu dama ba saboda tsoron abin
zai iya faruwa kowane lokaci.
Wasu Labarai
0 Comments