Talla

Yadda Wasu Maza Suka Duƙufa Turawa Mata Hotunan Batsa A Shafukkan Sada Zumunta

 Daga: Bello Hamisu Ida

Shafukan sada zumunta ko kuma dandalin sada zumunta shafi ne da ake amfani da su wajen sada zumunci tsakanin abokai da suka yi nisa ko suka haɗu a wannan kafa. Shafukka irinsu Fesbuk da Tiwita da Instagram da TikTok ta Telegaram da sauransu suna taka muhimmiyar rawa wajen sada zumunci. Cikin sauƙi mutum kan san wanda bai sani ba ta hanyar amfani da waɗannan shafukka, da zaran an ga wanda ya cancanta ayi abota da shi sai a tura masa saƙon son zama abokai.

Amma wani abun takaici da ban haushi shi ne, yadda wasu maza suka tuƙufa wajen neman mata a waɗannan shafukka. Da wasu mazan sun ga hotunan mata ko akawun mace sai su nemi yin ƙawance da ita, abu na gaba sai a nemi kusanci ta hanyar yin gaisuwa, idan kuma an samu dama sai a riƙa neman a tura hoto.

Wasu mazan kuwa da zaran mace ta karɓe su a matsayin abokai sai su fara kiranta kai tsaye, ko dai kira na jin murya ko kuma kira na ganin fuska wato bidiyo, a hankali sai su fara neman sanin inda mace take musamman idan ta bada haɗin kai.

Wata mata ta sanar da Arewa News cewa, yanzu haka ta bar amfani da akawunta na fesbuk saboda yadda maza suka yi mata ca, wasu kuma suna tura mata hotunan batsa ba tare da saninta ba. Wani abun takaici kuma mafi yawan masu turo mata irin hotunan batsa, samari ne ‘yan bana bakwai waɗanda basu wuce shekara ashirin zuwa talatin ba.

Akwai wani saurayi ɗan shekara ashirin da huɗu da ya taɓa ɗaukar lambar wata ma’aikaciyar Arewa News a cikin wani dandali na watsaf, bayan ya yi mata sallama, sai ya kirata da waya, duk da yake bata ɗauka ba, amma sai ya ci gaba da kiranta. Da ya tabbatar da cewa bata ɗauka sai ya fara turo mata hotunan batsa da bidiyo na batsa. Ta fara yi masa faɗa da nasiha, daga ƙarshe sai ya ce, ai wata mace ce ta koya masa aikata masha’a a kafar sada zumunta. Tun kuma daga lokacin sai ya maida hankali wajen aikata masha’a a kafar sada zumunci kuma abun ya zama jini kusan kullum in bai aikata ba, ba ya samun kwanciyar hankali. Amma da Arewa News ta bi diddiƙin matashin sai ta fahimci cewa ƙarya ya ke yi, babu wata mace da ta koya masa aikata irin wannan masha’a a kafar sadarwa, yana dai shirya ƙarya ne don ya biya buƙatarsa.

Haka kuma, Arewa News ta samu labarin mutuwar auren wata mata, bayan mijinta ya ga wasu hotunan batsa da wani ya turo mata ba tare da saninta ba, da farko mijin ya ɗauka tana biyewa mutumin ne a kafar sadarwa inda suke aikata fasiƙanci, amma da Arewa News ta bi diddiƙin saƙonin da mutumin ya riƙa turawa sai aka gano cewa matar babu ruwanta, mutumin ne yake ƙoƙarin jawo hankalinta ta hanyar turo mata hotunan batsa.

Akwai wani mutumi da Arewa News ta samu labarinsa, ɗan asalin Jihar Gombe wanda ya shahara sosai wajen neman mata a kafar sadarwa ta Fesbuk, da zaran ya ga mace na ɗora hotunanta a shafin sai ya bita ya yi mata saƙon gaisuwa, a hankali sai ya nuna cewa aurenta zai yi, da zaran ta bada kai ɓori ya hau, sai ya buƙaci da su haɗu, to daga haɗuwar ne yake fitowa a mutum ya yi fasiƙanci da ita.

Akwai yare ma na musamman da mazan suke yi don su tabbatar da cewa macen ‘yar hannu ce ko sabon shiga ce, wasu lokutan za a ji mazan na cewa cikin saƙo, ‘Turo mani hotuna masu zafi’, ko su ce, ‘in kira bidiyo kall in gan ki’, ko kuma su ce, ‘kai wannan riga taki haka, ina ma ace zan ga abinda ke cikinta’ ko kuma su ce, ‘nuna mani yadda ki ke barci’ da dai sauran ɓoyayyun kalamai da suke amfani da su.

Wasu mazan kuwa, sukan fito a mutum su yi kalaman batsa tare da tura hotuna ko bidiyo na batsa ga duk macen da suka samu ta karɓe su ko ta yi masu magana.

Kafofin sada zumunta dai sun zama wasu irin tsani dake taimakawa wajen taɓarɓarewa rayuwa. Kodayake, Malamai da sauran al’umma suna taimakawa sosai wajen wayarwa matasa kai na yadda za su yi amfani da kafar ta hanya mai kyau.   

Wasu Rahotanni

  1. Bayan Rashin Lafiyar Maryam Yahaya Sai Kuma Me Ya Faru Da Ita
  2. Yadda Mata Ke Tallata Tsiraici A TikTok da Instagram
  3. Wane Mataki Zaku Dauka Inda Kuka Kama Wanda Ya yiwa Diyarku Fyade

Post a Comment

0 Comments