Talla

Yadda Mata Ke Tallata Tsiraicinsu A Manhajar TikTok da Instagram

Daga: Bello Hamisu Ida

Kafofin sada zumunta na taka muhimmiyar rawa wajen gurɓacewar tarbiyya musamman tarbiyyar yara ƙanana da mata da matasa, inda suka duƙufa wajen tallata tsiraicinsu a kafar sadarwa musamman a manhajar Tiktok da Instagram. Kodayake masu ƙirƙirar manhajojin basu ƙirƙiri fasahar ba don yaɗa baɗala, sun yin don sada zumunci shi yasa aka fi kiran manhajojin da sunan dandalin sada zumunci. Mutane kan ƙirƙiri akawu a cikin shafukan sannan su saka hotunansu tare da neman abokai waɗanda za su riƙa tattauna maudu’ai da dama masu muhimanci da ilmantarwa.

Amma wasu daga cikin matasa musamman mata dake Arewacin Najeriya sukan yi amfani da kafar wajen yaɗa hotuna da biyoyin tsiraicinsu. Akwai akawu da dama na mata da maza da waɗanda aka ƙirƙira da nufin yaɗa wasu maudu’ai amma sau da yawa zaka samu masu wannan akawun sukan yi amfani da waɗannan akwaun a dandalin sada zumunta wajen ɗora hotunan tsiraici da batsa, wasu kuma su kan ɗora bidiyon tsiraicinsu ko na ƙawayensu ko ma na wasu can daban da basu san an samu hotuna ko bidiyon tsiraicinsu ba.

Wasu samarin musamman ‘yan mata sukan ɗora hotuna ko bidiyo cikin ɗagawa da ƙoƙarin nuna kyawonsu, wasu matasan kan yi amfani da kafar sadarwa kamar TikTok da Instagram  ta hanyar da ba ta dace ba, labarin wata matar aure da ta kama mijinta ya na ɗaukar hoton al’aurarsa don aika wa wata abokiyarsa a kafar sada zumunta ya ja hankali. A kan samu ire-iren waɗannan mazaje da mata, wasu mazajen kan buƙaci abokansu na kafar sadarwa su turo masu hotunan tsiraicinsu, cikin shashanci kuma sai ƙawayen su tura masu, musamman dai mata masu son nuna kyawunsu don su birge abokansu, ko don su saida tsiraicinsu ko kuma don su nemi wani abun duniya da tsiraicinsu.

Idan muka yi karambanin buɗe akawu na Tiktok ko Instagram da sunan mace, za mu sha mamakin yadda maza za su riƙa ribibin son zama abokanmu, kuma da zaran an fara fira babu abinda mazan suka fi so sai su ga tsiraici ko ta hanyar tura masu ko kuma ta hanyar ganin wanda aka ɗora ko dai hoto ko kuma bidiyo. Wasu lokutan abokan za su buƙaci a tura masu hoton mace don su ga ko wacece, idan suka samu wannan damar gaba kaɗan sai su fara roƙo a tura masu hotunan tsiraici.

Sau da yawa kuwa, a kan samu cewa mata ne mamallaka akawun, kuma su ne da kansu ke ɗora hotunansu na tsiraici, kuma duk sanda wani ya buƙaci a tura masa tsiraici su kan ɗauka su tura, wasu matan ma ko ba a roƙa ba sukan ɗora a bangon shafinsu don abokansu su gani kyauta.

Kamar misalin ayaba ce, da wadda aka cire wa ɓawonta da kuma wacce ba a cire wa ɓawo ba, kamar misalin kumfa da aka kaɗa zuwa gobe kuma ya kan narke ya koma kamar ba a kaɗa shi ba, kamar dai misalin rayuwa cikin samartaka ne da kuma rayuwa cikin tsufa. Idan an kula da wannan za a ga cewa suturtawa da ɓoye jiki da rashin bayyana tsiraici shi ne cikamakon kyakyawar rayuwa. Ita kuwa wannan kafa da aka ƙirƙira an ƙirƙire ta ne da wata manufa, amfani da kafafen ta kyakyawar hanya zai taimaka sosai wajen ingata rayuwa da samar da al’umma mai cike da tarbiyya. 

Wasu Rahotanni

    1. Shin Bestie Kwarto Ne?
    2. Yadda Mata Ke Tallata Tsiraicinsu A Manhajar TikTok da Instagram
    3. Wane Mataki Zaku Ɗauka Idan Ku Ka Kama Wanda Ya Yi Wa Ɗiyarku Fyaɗe?

Post a Comment

0 Comments