Talla

Wasiƙar Soyayya, Yanmata da Samari

Daga: Fadar Masoya

Shin ko za ku iya turawa masoyanku irin wannan wasiƙun? 

Haƙiƙa wasiƙar soyayya wasiƙa ce da masoya ke rubuta kalaman su cikin salo da fikira da jan hankalin masoyi cikin rubutu. Wannan dalilin ne yasa ake ƙayata wasiƙar da kwalliya cikin adon rubuce.

Haka kuma kowace irin wasiƙa ce matuƙar ta soyayya ce to wajibi ne a ke aiwatar da tsarin kalamai a cikinta don hakan ya zama sigar farkon nishaɗantar da zuciyar masoyi wanda aka rubutawa. Ita kawai ana ƙayatata ne da muhimman zantuka na birgewa da nishaɗi ga mai karantawa.

Misali wasiƙar soyayya:

Wasiƙar neman amincewa ga masoyiya,

 Zuwa gare ki sarauniyar masoya, matsayin girma da jinjinar ƙasaita su kasance a gare ki, ya mai cikakken iko a cikin fadar masoyan asali. Da fatan walwala da nishaɗin zuciya su ne fasalin farko abinda zai fara bayyana yayinda ki ka yi tozali da wannan saƙo nawa zuwa a gare ki, haka ne ya sa na ɗauki alƙalami da takarda gami da buɗe ƙofofin taskar yabo da fatan alkairi cikin azanci da kyakkyawar niyyar samun kusanci ga kyakkyawan zuciyarki.

 Tallafi da agajinki shi ne babban dalilin rubuto wannan farar wasiƙa don samun tabbacin cikon gurbin muhalli a cikin fadar zuciyarki, na daɗe ina ɗaukar ɗamarar shirin yin rarrafe da kwarin gwiwa don ki ɗauke ni ki saka cikin jerin masoyanki na asali, fatana ya kasance tausayina zai zamo hujjar kore dukkanin shakkar amincewarki a kan tafarkin soyayyata.

Ki huta lafiya

Bissalam.

Haka kuma ana iya samun bambancin wasiƙar soyayya kamar yadda wasu 'yanmata suke rubutawa samari don neman amincewa.

 Misali:

Zuwa gareka Basaraken Masoya,

 Sallama cikin amincin Allah da rahamarsa su tabbata a gareka kyawun Anita, tabbacin nagarta da matsayi da ɗaukaka su ƙara tabbata tare da kai ya Basaraken Masoyan Duniya.

Jinkirin ɗaukar damarar samun hanyoyin da zan isar da saƙonnina zuwa gareka shi ne ya zamo maƙasudin dalilin rubuta wannan takarda tawa a gareka jigon masoyan asali.

 Haƙiƙa kai sarki ne kuma jagayya a cikin rundunar ma'abota soyayya hakan ne ya sa ka zamo shugaban masoya ma'abota so da ƙaunar juna. Zan so ace na kasance ajin farko a cikin dubban masoyanka ko don in ƙara tabbatarwa duniya cewa kai cikakken masoyi ne na musamman idan ka nuna tausayawa ga zuciyar da ta marairaice a kan soyayyarka.

 Wannan shi ne dalilin farkon rubutun alƙalamina cikin azanci gami da fatan samun nasarar karɓuwa ga amintacciyar zuciya.

Ka huta cikin kyakkyawan yanayi.

Bissalam.

Bayan waɗannan wasiƙu da suka tabbata a matsayin neman amincewa a tsakanin samari da 'yanmata wannan ya na iya zama babbar hanyar isar da saƙon zukata cikin sauƙi. Duk da cewa wasu sukan rubuta wasiƙa ne don ƙarin danƙon soyayya a tsakaninsu.

Post a Comment

0 Comments