Daga: Muhammad Abdallah
BAUCHI, NAJERIYA — Wani yaro da ya fito daga ƙaramar huumar Ningi wanda bai wuce shekara goma sha huɗu ba ya kashe kansa, rundunar ƴansandan jihar Bauchi ta tabbatar da mutuwar wannan yaro.
Mai
magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Bauchi Ahmed Wakil ya tabbatar da
faruwar al’amarin inda ya ƙara da cewa, yaron ya kashe kansa ne ta hanyar
rataye kansa a wani kangon ɗaki.
Mahaifin
yaron ne ya sanar da ƴansanda abinda ya faru da ɗansa kafin daga bisani su je
inda gawar yaron take, kafin yaron ya rasu, yana fama da taɓin ƙwalwa rashin
lafiyar da ake tsammani ta yi silar mutuwarsa.
Ɗansanda Ahmed
Wakil ya ƙara da cewa,
“Bayan sanar da
ƴan sanda nan take jami'anmu suka inda al’amarin ya faru kuma aka ɗauki yaron
zuwa babbar asibitin Ningi amma aka tabbatar da ya mutu.”
Rundunar
ƴan sandan Bauchi ta ce ta ƙaddamar da bincike domin gano dalilin da ya sa
yaron ya kashe kansa.
Ana yawan samun
mace-mace a ɗan lokuttan nan ta hanyar kashe kai lamarin da yake jan hankalin
duniya.
Wasu Labarai
0 Comments